Wakilan kungiyar shugabannin kasashen gabashin Afirka ta EAC, sun dage taron da suka shirya gudanarwa a ranar Laraba, game da yanayin da ake ciki a kasar Burundi, biyowa bayan wani yunkurin juyin mulkin soji da ya auku a kasar.
Wata sanarwa da babban daraktan sadarwa na kungiyar dake Dares Salaam na kasar Tanzaniya ya fitar, ta ce, EAC ta yi Allah wadai da yunkurin juyin mulkin, wanda a cewar sanarwar, ba zai haifar da komai ba sai kara dagula al'amura a kasar.
Yayin wani taron ganawa da manema labaru da suka gabatar, shugaban kasar Tanzaniya Jakaya Kikwete, da shugaban kungiyar ta EAC, kuma shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, da Uhuru Kenyatta na kasar Kenya, sun bayyana cewa, juyin mulki ba zai zamo hanyar warware rikicin siyasar kasar ta Burundi ba.
Tashe-tashen hankula sun barke ne a kasar tun bayan da shugaba Pierre Nkurunziza ya bayyana bukatarsa ta tsayawa takara, a babban zaben kasar dake tafe a karo na uku, lamarin da ya haifar da tarzoma da asarar rayukan mutane 10, baya ga wasu 40,000 da suka tsere zuwa kasashen Rwanda da Tanzania. (Saminu)