Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU a ranar Lahadin nan ta tura wata tawaga ta musamman zuwa kasar Burundi domin samo mafita a tashin hankali da ta fada, kamar yadda wata sanarwa daga cibiyar kungiyar a Adis Ababa ta bayyana.
Kungiyar tun ba yau ba ta jaddada kirarta a kan bukatar tattaunawar sulhu a cikin al'amarin da yake neman kara muni a kasar.
A karkashin jagorancin Edem Kodjo, tsohon babban sakatare na kungiyar hada kan kasashen Afrika OAU, kuma tsohon firaministan ministan kasar Togo, yanzu haka ma mamba a kwamitin dattawa na AU, tawagar za ta gana da mahukuntar kasar Burundi, sannan da sauran masu ruwa da tsaki da suka hada da jam'iyyun siyasa, kungiyoyi masu zaman kansu da shugabannin addinai.
Tawagar kuma za ta gana da wakilan 'yan kasashen waje dake Bujumbura, babban birnin kasar, kuma za ta yi aiki kafada da kafada da manzon musamman na MDD game da batun yankin babban tafki Sa'id Djinnit duk a cikin aniyar MDD da kungiyar ta AU wajen samar da zaman lafiya da tsaro.
Burundi ta fada cikin rikici ne saboda shugaban kasar mai ci yanzu Pierre Nkurunziza ya bukaci sake darewa karagar mulkin kasar a karo na uku, ya zuwa yanzu kuma a kalla mutane 14 sun rasa rayukasu, wassu da dama kuma sun samu raunuka tun daga lokacin da rikicin ya fara a ranar 25 ga watan Afrilu. (Fatimah)