A jiya ne kungiyar kasashen da ke gabashin Afirka (EAC) ta aike da wata tawaga mai kunshe da ministocin harkokin wajen kasashe 4 zuwa kasar Burundi don sasanta rikicin siyasar da ke ci gaba da ruruwa sakamakon kokarin da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ke yi na neman wa'adi na uku na shugabancin kasar.
Shugaban kungiyar ta EAC, kana shugaban kasar Tanzaniya Jakaya Kikwete ya bayyana cewa, aikin tawagar shi ne gano dalilan rikicin da kuma hanyoyin da suka kamata a dauka na magance shi, a wani taron gaggauwa da kungiyar za ta kira na shugabannin kasashe mambobin kungiyar don tattauna matsalar siyasar kasar ta Burundi bayan kammala aikin tawagar.
An kuma ruwaito shugaba Kikwete na cewa, za a magance rikicin kasar Burundi ne ta martaba kundin tsarin mulki da na zaben kasar. Ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su ceto kasar Burundi daga fadawa cikin rikici.
Tun a ranar 26 ga watan Afrilu ne rikici ya barke a kasar Burundi, kwana guda bayan jam'iyyar CNDD-FDD mai mulkin kasar ta tsayar da shugaba Nkurunziza a matsayin mutumin da zai yi mata takara a zaben shugaban kasar na watan Yuni.
A jiya Talata kuma kotun tsarin mulkin kasar ta yanke hukuncin cewa, Nkurunziza zai iya tsayawa takara a zaben shugaban kasar da ke tafe, matakin da ake ganin zai iya kara rura wutar tashin hankali a kasar. (Ibrahim)