Kamfanin zirga-zirgan jiragen sama na Turkiya wato THY ya musanta zargin jigilar makamai zuwa Nigeria.
Wata sanarwa da ta fito daga kamfanin THY ta ce, kamfanin bai yi jigilar makamai zuwa kasashen da ba su da cikakkun shugabanci ko kuma wadanda ke cikin yaki.
A ranar Talata ne, aka nadi tattaunawar da Mehmet Karatas, babban daraktan kamfanin THY ya yi da Mustafa Varank, mai ba da shawara ga firaminista Recep Tayyip Erdogan a wani shafin intanet, game da jigilar makaman da kamfanin ya yi zuwa kasar Najeriya.
Kamfanin THY ya kara da cewa, yana aiki ne bisa tsarin jigilar makamai da na daukar kayayyaki kamar yadda kungiyar sufurin jiragen kasa ta duniya ya tanada. (Suwaiba)