in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An maida hankali kan batun dakile yaduwar cututtuka a taron kara wa juna sani tsakanin Sin da Amurka
2015-05-13 17:05:29 cri

Kungiyar sada zumunta da kasashen waje ta jama'ar kasar Sin, da jami'ar koyon aikin gona da masana'antu ta Texas dake kasar Amurka, sun kira taron karawa juna sani game da huldar dake tsakanin Sin da Amurka karo na 6 a ranar Talata a birnin Houston na kasar Amurka, inda aka tattauna wani babban jigo na "Cututtuka masu yaduwa a duniya, shirin da ake yi da tinkarar matsala."

Mahalarta taron sun hada da masana, da kwararru a fannin hana yaduwar cututtuka fiye da 400 daga kasashen Sin da Amurka, inda suka yi musayar ra'ayi dangane da shirin da ake yi, na tinkarar barkewar annoba a kasashe masu tasowa, da fasahar hana yaduwar cutar Ebola, da rawar da ya kamata kamfanoni su taka a kokarin dakile cututtuka, da dai sauran fannoni daban daban.

A cewar mista Xu Kuangdi, shugaban kungiyar sada zumunta tsakanin Sin da Amurka, a sabon karnin da muke ciki ana fuskantar karin kalubuloli, "Abin da ake tattaunawa a wannan taron da muke yi, ya shafi aikin kiwon lafiyar jama'a a kasashe daban daban musamman ma kasashe masu tasowa, da manufofin da kasashen suke dauka don tinkarar wasu matsaloli a wannan fanni, a kokarin dakile cututtuka masu yaduwa, ga misali cutar Ebola da aka samu yaduwarta a yammacin Afirka, dukkansu sun zarce huldar dake tsakanin Sin da Amurka, wato sun shafi kasashe daban daban, tare da bukatar a warware su cikin gaggawa."

A cewar Xu, Sin da Amurka sun dade suna hadin gwiwa a fannin aikin jinya da kiwon lafiya. Sa'an nan a shekarun baya, kasashen 2 sun yi ta kokarin habaka hadin gwiwar su, lamarin da ya yi matukar amfani ga kasashen 2.

Ga misali a kokarin dakile cutar AIDS ko SIDA, hukumomin kasashen 2 sun yi nazari game da bangarori daban daban, tare da samun hakikanin ci gaba, bayan da suka kulla yarjejeniyar hadin gwiwa a shekarar 2002.

Haka zalika, bayan da aka samu barkewar annobar Ebola a yammacin Afirka, kasashen Sin da Amurka sun yi musayar ra'ayi sosai game da yadda za a tinkari annobar, haka kuma sun kalubalanci sauran kasashe daban daban a taron kungiyar G-20, wajen bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban a kokarin kau da cutar.

A cewar mista Xu, kamata ya yi, kasashen Sin da Amurka, bisa matsayinsu na kasashe masu karfin tattalin arziki, su ba da gudummawa ga aikin wanzar da zaman lafiya, da tabbatar da ci gaban rayuwar dan Adam. Saboda haka ya yi kira da a kafa wani asusun tinkarar cututtuka masu yaduwa, don tallafawa kasashe masu tasowa.

A nasa bangare, Neil Bush, da ga tsohon shugaban kasar Amurka George Herbert Walker Bush, ya amince da shawarar mista Xu Kuangdi, yana mai cewa, "A fannin dakile cututtuka masu yaduwa, da kokarin taimakawa sauran kasashe tinkarar wannan matsala, hadin gwiwar da ake yi tsakanin Sin da Amurka zai zama abin koyi ga sauran kasashe duniya."

Ban da haka, a nata bangare, shugabar kungiyar sada zumunta da kasashen waje ta jama'ar kasar Sin madam Li Xiaolin, ta ce za a iya habaka hadin gwiwar kasashen 2 zuwa karin fannoni daban daban. Haka kuma za a tattauna karin batutuwa a taron kara wa juna sani dangane da huldar dake tsaknin Sin da Amurka, kamar su ingancin abinci, da kiyaye muhalli, da dai makamantansu. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China