in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan tsaron kasar Sin Chang Wanquan ya gana da takwaransa na Amurka Chuck Hagel
2013-08-20 15:10:57 cri

Ministan tsaron kasar Sin Chang Wanquan wanda yake ziyara a kasar Amurka ya gana da takwaransa na Amurka Chuck Hagel a birnin Washington D.C.,hedkwatar mulkin kasar, inda bangarorin biyu suka yi shawarwari suka kuma cimma matsaya daya da dama kan wasu manyan batutuwa, ciki hadda dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da sojojinsu, wasu batutuwa dake da nasaba da kasashen biyu, da na shiyya-shiyya, kana da tsaron Intanet da sauransu.

Ministan tsaron kasar Sin Chang Wanquan ya tashi a ran 16 ga wata don kai ziyara a kasar Amurka, inda daya bayan daya ya ziyarci hedkwatar kwamandan sojin kasar mai kula da harkokin yankin tekun Pacific wato PACOM, da ta kwamandan sojin kasar mai kula da tsaron yankunan kasar wato USNORTHCOM, da kuma ta kwamandan tsaron sararin sama na nahiyar Arewacin Amurka wato NORAD. Sannan nan ya gana da takwaransa Chuck Hagel a ran 19 ga wata a birnin Washington D.C.. Bayan ganawarsu, Mr.Hagel ya ce,

"Mun cimma nasara sosai cikin ganawar da muka yi, yayin ganawar, na nanata kokarin da Amurka take yi wajen raya wata dangantaka mai yakini a tsakaninta da kasar Sin yadda ya kamata, wadda za ta ba da taimako wajen samun zaman lafiya da na karko a yankin Asiya da na tekun Pacific, sa'i daya kuma za ta kawo amfani wajen samun zaman lafiya da wadata a kasashen Amurka da Sin a karni na 21."

A cikin ganawar, Chang Wanquan da Hagel sun tattauna kan wasu manyan batutuwan da ke da nasaba da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da sojojinsu, lamuran da ke shafar muradun bangarorin biyu, da na shiyya-shiyya, kana da tsaron Intanet da sauransu, sannan nan sun cimma matsaya daya da dama.

Da farko, bangarorin biyu sun amince da aiwatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma yayin da suka ganawa da juna a gandun gona na Anneburg. Kuma za su dukufa kan raya dangantakar dake tsakanin sojojin kasashen biyu zuwa wani sabon mataki.

Na biyu kuwa, bangarorin biyu sun amince da kara tuntubar juna da zurfafa shawarwari a tsakanin sojojinsu, domin kara amincewa da juna. Amurka ta gayyaci babban hafsan-hafsoshin sojin 'yantar da jama'ar kasar Sin da ya kai ziyara a kasar Amruka a shekarar 2014, Sin kuwa ta gayyaci ministan tsaron kasar Amurka da ministan kula da yake-yake a teku da su kai ziyara a kasar Sin a shekarar 2014. Ban da haka, bangarorin biyu sun yarda da tattaunawa kan batun kafa wani tsarin tuntubar juna kan wasu manyan batutuwa a fannin soja, tare kuma da ci gaba da nazarin ka'idojin tabbatar da tsaron aikin soja na teku da na sama tsakaninsu.

Na uku, bangarorin biyu sun amince da cewa, sojojin kasashen biyu na da babban nauyi dake bisa wuyansu wajen kiyaye zaman lafiya da na karko a yankin Asiya da tekun Pacific, ya kamata su dauki matakan da suka dace cikin harkokin shiyya-shiyya, ta yadda za su inganta hadin gwiwa a tsakaninsu a wannan yanki yadda ya kamata, bisa tsarin shawarwari tsakanin bangarori daban-daban a yankin. Ban da haka, Sin za ta shiga atisayen soja cikin hadin kai na yankin Asiya da tekun Pacific na shekarar 2014 bisa gayyatar da aka yi mata.

Na hudu kuma, bangarorin biyu sun yarda da kara cudanya da hadin kansu a fannonin ba da taimakon jin kai, yaki da ta'addanci, yaki da 'yan fashin teku da kiyaye zaman lafiya, kuma sun yanke shawarar yin atisayen soja cikin hadin kai a watan Nuwamba na bana a Hawaii na Amurka ta fuskar jin kai, dadin dadawa a karshen wannan shekara za su tattauna kan batun ayyukan tsaro da ba da tabbaci ga aikin samar da guzuri.

Na karshe kuwa, bangarorin biyu sun amince da hadin kai a fannin takardun soja, da kuma kafa wani tsari a wannan fanni, bisa tushen taimakon da Sin ta baiwa Amurka wajen gano 'yan Amurka da suke bace.

Mr. Chang Wanquan ya kuma furta cewa,

"Dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka na cikin wani sabon zamani. Kafa wata sabuwar dangantakar dake tsakanin sojojin kasashen biyu zai taimaka wajen kara amincewar juna, tare kuma da kawar da wasu kalubaloli a fannin dabarun soja, har ma zai taimaka wajen kiyaye zaman lafiyar duniya da zaman karko a shiyya-shiyya. Sin na fatan kara hadin kai da Amurka domin aiwatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kara yin tattaunawa da mu'ammla da kuma hadin gwiwa tsakaninsu, da daidaita wasu matsaloli da bambancin ra'ayi tsakaninsu yadda ya kamata, a kokarin ciyar da dangantakar dake tsakanin sojojinsu zuwa gaba."

Bayan kammala ziyararsa a Amurka, Mr. Chang Wanquan zai je kasar Canada don ci gaba da ziyarar aikinsa. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China