in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake bude makarantun firamare da na sakandare a kasar Saliyo
2015-05-06 16:27:06 cri

Sakamakon sassautar yaduwar cutar Ebola, a tsakiyar watan da ya gabata, gwamnatin kasar Saliyo ta sanar da sake bude makarantun firamare da na sakandare a dukkan kasar, wadanda suka dakatar da darrusa har na tsawon watanni 9. Sake komowa makarantu da dalibai fiye da miliyan daya na kasar suka yi, yana da ma'ana kwarai ga wannan kasa da ta yi fama da cutar Ebola, daliban kasar ta Saliyo sun nuna imani da fata ga kasar.

Wasu daliban wani aji a wata makarantar sakandare dake yankin Freetown, hedkwatar kasar ta Saliyo ne suka rera wannan waka mai dadi , wWadda ba kullum aka saba jin ta ba. A cikin watanni 9 da suka wuce, sakamakon yadda cutar ke saurin yaduwa a cikin wannan karamar kasa dake yammacin Afirka, ta sanya ta ayyana dokar ta baci, inda aka rufe makarantun firamare da na sakandare fiye da 8000 da ke fadin kasar har illa masha-allahu, yayin da dalibai kimanin miliyan 1.8 suka koma gida don gudun kamuwa da cutar. A yanzu bayan shekara daya da wani abu da suka gabata da aka yi kokarin yaki da cutar, yanayin cutar Ebola da kasar ke ciki ya samu kyautatuwa, amma duk da haka kasar na ci gaba da dandana illar da cutar ta haifar a kasar. Saboda haka, tun daga ranar 13 ga watan Aflilu da gwamnatin ta sanar da sake bude makarantu ya zuwa yanzu, a cikin wadannan makwanni uku kashi 60 cikin 100 ne kawai na dalibai a zahiri suka koma makarantun, wadanda kuma suke ci gaba da tattaunawa kan batun cutar Ebola:

"Haka ne! Muna fatan komowa makaranta! Muna son saduwa da abokan karatunmu, muna son karatu, amma a sa'i daya muna tsoron cutar Ebola, hakika cuta ce mai ban tsoro. Yanzu mun san cewa, bai kamata a ci namun daji ba, ya kamata mu rika wanke hannunmu, mu kuma kula da tsaftar jikin mu, kada mu yi cudanya da wadanda suka kamu da cutar. Idan mun girma, muna son mu zama likitoci ko ma'aikatan jinya, domin kula da lafiyar sauran mutane."

Ko shakka babu, har yanzu ba a iya kawar da mummunan tasirin da cutar Ebola ta haifar wa kananan yara cikin gajeren lokaci a kasar ba. Amma sake bude makarantu yana da ma'ana sosai ga wannan kasa. A ganin Abdullah, wani malami a wata makarantar sakandare ta Freetown, daliban da suka sake komowa makarantu sun kara kwarin gwiwa ga kasarsu:

"Wannan ya ba mu kwarin gwiwa sosai. Dalibai sun dade ba sa makaranta sakamakon cutar Ebola, saboda haka, komowarsu makaranta ba ya nufin sake bude darrusa kawai, a waje guda ya baiwa dukkan kasarmu kwarin gwiwa wajen cimma nasarar yaki da cutar Ebola."

Manyan dalilan da suka sanya kasar Saliyo ta kasa yaki da cutar Ebola a wannan karo, su ne tsarin al'adar kiwon lafiya marasa kyau na zaman takewar al'umma, da kuma rashin fasahohin rigakafin cututtuka masu yaduwa. Bayan wannan bala'in, wadannan dalibai za su taka muhimmiyar rawa wajen tsara tsarin rigakafi da shawo kan cututtuka na kiwon lafiyar kasarsu a nan gaba. A wani shirin horaswa kan rigakafin cututtuka masu yaduwa, wani jami'in kula da harkokin kiwon lafiya a yammacin Freetown mista Paul ya bayyana wa dalibai da suka fito daga wurare daban daban cewa,

"Dalibai, har zuwa yanzu ba a shawo kan cutar Ebola ba. Wannan cutar ta yi kama da barawon dake boye, idan ba mu yi taka tsan-tsan ba, to za ta sake dawowa. Dabarun da za mu koya muku a nan, ina fatan za ku isar da su ga iyalanku da abokanku."

Darrusan da mista Paul ya ambata, sun kasance muhimman abubuwa dake cikin jerin shirye-shiryen ba da horo da tawagar koyar da dabarun kiwon lafiyar jama'a karo na 4 da kasar Sin ta turo zuwa kasar ta Saliyo. Wadannan daliban da suka sake komowa makarantu za su samu irin wannan horo. Shugaban tawagar mista Yin Zundong ya bayyana cewa,

"Muhimmin aiki da ke gabanmu shi ne, ba da horo ga malamai da dalibai game da matakan yin rigakafi da shawo kan cututtuwa. Ta hanyar horar da malamai da dalibai, iyayen dalibai ma za su koyi wadannan matakai ko dabaru daga wajen yaransu, daga baya kuma za su taimakawa daukacin al'ummar kasar. Mun yi imaninkiyasta cewa, za mu ba da horo ga mutane fiye da 6000." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China