in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Liberia ta sanar da samun kubuta daga mummunar cutar Ebola
2015-05-11 16:13:34 cri

A ranar 9 ga watan nan ne, yammacin nahiyar Afirka da mummunar cutar Ebola ta addabe shi ya samu wata babbar nasara, bayan ganin yadda kasar Liberiya da ta fi fama da cutar Ebola ta sanar da samun tsira daga cutar, bayan da aka kwashe kwanaki 42, ba tare da samun wani ya kamu da cutar a kasar ba. Wane irin karfi ne da kasar Liberia ta samu wajen cimma nasarar yaki da cutar Ebola? Kuma wane darasi ne duniya za ta samu daga babbar hasarar da kasar Liberia ta sha?

A farkon watan Maris na shekarar 2014, a ka fara gano wasu mutanen da suka kamu da cutar Ebola a yankin Lofa na kasar Liberia, wanda yake kusa da mafarin cutar a kasar Guinea, amma an kawar da cutar cikin sauri, hakan ya sa kasar Liberia ta sassauta sanya idon da take yi wa cutar. Daga baya, a watan Yuli, annobar ta barke bayan yaduwar cutar Ebola a wani asibitin da ya karbi wanda ya kamu da cutar daga kasar Saliyo. Francis Kateh, mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar Liberia kuma shugaban kwamitin kula da ayyukan ba zata da ke da nasaba da cutar Ebola na duk fadin kasar ya bayyana cewa,

"A tarihin da, cutar Ebola ta kan barke a kauyukan da ke dangun daji, wadda ta kan shafi mutane kalilan. Amma a wannan karo, an gano cutar a biranen da ake iya samun mutane masu dimbin yawa, wannan kuma wani muhimmin dalili ne da ya sa ba mu shawo kan cutar yadda ya kamata ba."

Sakamakon saurin yaduwar cutar Ebola, an fara gano mutane fiye da dari da suka kamu da cutar a ko wace rana, hakan ya sa gwamnatin kasar Liberia ta tura sojoji don datse yankunan da suka fi fama da cutar, har ma a birnin Monrovia, fadar mulkin kasar, an killace dukkan mutanen da ke unguwanni biyu, lamarin da ya haddasa dagiyar da aka nuna wa gwamnati, sai dai abin takaicin shi ne, duk da wannan, yawan mutanen da suka kamu da cutar Ebola ya ci gaba da karuwa cikin sauri.

Ganin haka, yasa gwamnatin Liberia ta fara neman sabuwar hanya, bayan makwanni biyu kawai, an tilasta a kawar da matakin datsewa. Mr. Kateh ya furta cewa,

"hakikanin abu ya sheda cewa, karfin soja da kuma matakan nuna karfin tuwo ba su iya shawo kan cutar Ebola ba. Abin da ya kamata mu yi shi ne a yi kira ga jama'a da su ba da kariya daga cutar da kansu. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da jama'a su san muhallin zamansu sosai, idan sun iske wanda ya kamu da cutar, cikin gaggawa su buga waya ga cibiyar kula da lamuran ba zata. Hakan ana iya ganin cewa, yadda dukkan al'umma suka sa hannu a cikin wannan aiki ya zama wani muhimmin aiki wajen samun waraka daga cutar Ebola."

Yayin da kasar Liberia ke kokarin fama da wannan mummunar cutar, dimbin kungiyoyin ba da agaji na kasa da kasa sun fara isa kasar, wadanda suka karfafa kwarin gwiwar al'umma kasar sosai wajen ci gaba da shawo kan cutar Ebola. A cikinsu kuwa, kasar Sin ta zama kasa da ta fi samar da taimako a cikin lokaci. Mr. Kateh yana mai cewa,

"bayan barkewar cutar Ebola, da farko mun samun taimako daga wajen kasar Sin, wadda ta karfafa zuciyarmu sosai. Kasar Sin ta kafa asibiti mai kyau a kasar Liberia don masu fama da cutar Ebola. Ban da samar mana na'urorin jiyya masu kyau, likitocin kasar Sin su ma sun kware sosai wajen aiki, abin da ya sa suka warkar da mutane masu dimbin yawa da suka kamu da cutar Ebola. Gudummawar da suka bayar ta kyautata fatan mu wajen fama da cutar."

Bisa kokarin da aka yi a kasar Liberia, bayan watanni uku, halin da kasar ke ciki wajen fama da cutar ya samu kyautatuwa, yawan mutanen da suka kamu da cutar ya ragu sosai, har ma ya zuwa ranar 9 ga watan nan, kasar ta cimma nasarar yaki da cutar Ebola, bayan da aka kwashe kwanaki 42, ba tare da samun wani ya kamu da cutar a kasar ba.

A cikin wannan tashin hankali na barkewar cutar Ebola da ya fi tsanani a tarihi, mutanen da suka mutu a kasar Liberia ya kai 4,716, yayin da wannan jimilla ta zarce 11,000 a duk duniya. Babu shakka, Liberia da sauran kasashen duniya sun yihasara sakamakon cutar, kuma sun samu wani darasi mai daraja. Mr. Kateh ya ce,

"Cutar Ebola ta yi kama da wani malamin duba, wadda ta jarraba tsarin kiwon lafiya na kasar Liberia. Ta wannan jarrabawa, mun gano kasawa da kuma gibin da ke tsakaninmu da saura. Yanzu lokaci ya yi da muka yi tunani domin samun darasi daga wajen cutar Ebola."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China