in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matasa da 'yan matan Sin da Afirka sun halarci bikin da kamfanin Startimes ya shirya a nan Beijing
2015-05-05 16:40:43 cri

A yayin da ake murnar bikin ranar matasa da 'yan mata na kasar Sin karo na 96 a ranar Litinin 4 ga wata, wasu matasa da 'yan mata na kasar Sin da kasashen Afirka sun taru a kamfanin Startimes dake nan birnin Beijing, don nune-nunen rera wakoki da raye-raye, inda suka yi musayar ra'ayi tsakanin juna.

Emeka Anochirinye, wani matashi ne dan Najeriya, wanda ya yi jawabi a madadin ma'aikata matasa da 'yan mata na kasashen Afirka dake aiki a kamfanin Startimes, ya ce, a matsayinsa na matashi da ke zama cikin duhu dangane da abin da zai kasance a nan gaba. Koda ya ke shi ya yi sa'a, ganin yadda ya samu damar aiki a kamfanin Startimes. Babban taken kamfanin na "sanya ko wane iyalin nahiyar Afirka samun damar kallon shirye-shiryen telabijin irin na zamani" ya burge shi sosai, abin da ya taimaka masa cimma burinsa. A cewarsa, "Matasa da 'yan mata suna taka muhimmiyar rawa a yayin da ake hulda tsakanin kasashen Sin da Afirka. Na tuna a baya shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba bayyana matasa da 'yan mata a matsayin maballai. Ya ce idan ba a sanya maballi daya cikin kofarsa daidai ba, to sauran maballan ma za su gamu da kuskure."

Ya yi kira ga dalibai 'yan Afirka dake karatu a nan kasar Sin, da matasa da 'yan mata wadanda ke aiki a kamfanonin kasar Sin dake kasashen Afirka, da su yi kokarin tabbatar da zumuncin dake tsakanin kasashen Sin da Afirka, kamar yadda maballai ke taimakawa wajen hada bangarorin tufafi waje guda. Haka zalika, ya bukaci da a kara mai da hankali kan musayar ra'ayi a fannin al'adu tsakanin kasashen Sin da Afirka, ban da sa lura ga huldarsu a fannin tattalin arziki da cinikayya.

A nata bangare, wakiliyar ma'aikata samari da 'yan mata na asusun raya kasashen Sin da Afirka, Liu Xiaoxi, ta bayyana abin da ta gane ma idanunta yayin da take ziyara a kasashen Afirka, game da ayyukan da suka kunshi jarin da asusunta na raya kasashen Sin da Afirka ya zuba, ta ce, "A Shekarar da ta gabata, na je kasar Mozambique a karon farko, inda na ziyarci wani babban kanti na kamfanin Startimes dake can, kantin da asusun raya kasashen Sin da Afirka ya zuba jari ciki. A wajen, na ga yadda ma'aikata 'yan Mozambique suke sanye da kaya iri daya, inda suka karbi baki bisa wani nagartaccen tsari, na ji tamkar ina cikin wani kamfanin sadarwa dake nan kasar Sin. Amma dukkan ma'aikatan 'yan kasar Mozambique ne. Wannan shi ne karon farko da na gane ma idanuna wani sauyin yanayin da aka samu a wata kasar dake Afirka, bayan da kamfanonin Sin suka yada tsare-tsarensu a can."

Jawaban da wakilan ma'aikata 'yan kasashen Sin da Afirka na kamfanonin kasar Sin suka yi, sun karfafa niyyar da dalibai 'yan kasashen Afirka suke da ita, ta kokarin karfafa zumunta tsakanin kasashen Sin da Afirka. Kamar yadda, Yang Guang, wani dalibi dan kasar Tanzania dake karatu a jami'ar kimiyya da fasaha ta birnin Beijing, ya bayyana cewa,

"Yayin da ake kokarin raya huldar hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka, kamata ya yi, samari da 'yan mata su kara taka muhimmiyar rawa. Don haka ina son yin kokari tare da abokaina 'yan kasar Sin, don zama jakadun juna, wadanda za su taimakawa raya hulda tsakanin bangarorin 2. "

A karshen shekarar bara ne aka gudanar da wannan biki karkashin jagorancin asusun raya kasashen Sin da Afirka, wanda a karon farko ya gudanar da bukukuwa a jami'o'i, da kamfanoni, da dai sauransu, da zummar karfafa dankon zumunci tsakanin samari da 'yan mata na bangarorin 2, da share hanya ga hadin gwiwa da musayar ra'ayi da za a yi a nan gaba, musamman ma a fannonin tattalin arziki da al'adu. Sa'an nan bikin da aka yi a ranar Litinin, shi ne irinsa na farko da aka shirya a cikin wani kamfani. Hakan na nufin cewa ana kokarin samar da dama ga samari da 'yan mata don su cika burin da suka sanya a gaba. Har wa yau kuma, an nuna musu guraben ayyukan yi da za su iya samu a nan gaba.

Dangane da haka, Yang Aiwu, mataimakin shugaban asusun raya kasashen Sin da Afirka, ya ce, "An shirya bikin ne, don sanya kamfanonin mallakar kasar Sin da na sauran kasashe, da su samar da guraben aikin yi ga samari da 'yan mata na kasar Sin da kasashen Afirka, ta yadda za su samu damar nuna kwarewarsu tare da cika burinsu na rayuwa." (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China