in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya kai ziyara a kasar Malawi
2015-05-13 11:06:29 cri
Mataimakin shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Ping ya kai ziyara a kasar Malawi tare da 'yan rakiyarsa daga ranar 10 zuwa ranar 12 ga wannan wata. A yayin ziyararsa, Mr. Zhang Ping ya gana da shugaban kasar da kuma shugaban majalisar wakilan kasar Richard Msowoya

A yayin ganawar, Mr. Zhang Ping ya mika gaisuwar shugabannin kasar Sin tare da bayyana cewa, hadin gwiwar kasashen Sin da Malawi na fuskantar sabon zarafi, abin da ya sa kasar Sin ta sa kaimi ga kamfanonin kasar wajen zuba jari a kasar Malawi, kuma tana son ba da taimako bisa iyakarta domin bunkasa kasashen biyu tare da kawo moriyar jama'arsu gaba daya.

Ya ce majalisar wakilan jama'ar kasar Sin tana son kara tuntubar majalisar wakilan kasar Malawi domin ba da gundumawa ga bunkasuwar huldar kasashen biyu.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China