in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya yi fatan shugaban Uganda zai taimaka wajen warware rikicin kasar Burundi
2015-05-06 16:25:02 cri
Babban magatakardar M.D.D. Ban Ki-Moon, ya bayyana fatan ganin shugaban kasar Uganda Yoweri Kaguta Museveni, ya taimaka wajen cimma nasarar wanzar da zaman lafiya a kasar Burundi.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar Uganda ta fitar a jiya Talata, ta ce Ban Ki-Moon ya fadi hakan ne yayin ganawarsa da Museveni a ranar Litinin a hedkwatar M.D.D.

Yayin da yake karfafa bukatar taimakawa Burundi wajen warware rikicin dake addabar ta, a sa'i daya kuma, Ban Ki-Moon ya jinjinawa kokarin da Museveni, da sauran shugabannin Afirka ke yi wajen samar da zaman lafiya, da wanzuwar demokuradiyya a kasar ta Burundi.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China