Har wa yau shugabannin biyu sun jaddada aniyar hade manufar Sin ta bunkasa yankunan hanyar Siliki, da manufar Rasha ta raya hadin gwiwar Turai da nahiyar Asiya a fannin tattalin arziki.
Da yake tsokaci game da hakan, shugaba Xi ya bayyana jin dadin sa don gane da halartar bikin cika shekaru 70, da Rasha ta cimma nasarar kare kanta daga 'yan facist, yana mai cewa sadaukarwa da kasashen Sin da Rasha suka yi a yayin yakin duniya na biyu, abu ne da ba za a taba mantawa da shi a tarihi.
A nasa bangare shugaba Putin ya yi na'am da ra'ayain shugaba Xi, ya na mai cewa kasashen biyu ba za su taba amincewa da duk wani yunkuri na sauya tarihi ba. Kaza lika za su ci gaba da kushe manufar bayyana alfanun amfani da karfin tuwo, ko mulkin danniya, da ma duk wasu hanyoyi da masu ra'ayin mulkin mulaka'u ke yayatawa. (Saminu)