in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Kazakhstan za su bunkasa dangantakar manyan tsare-tsare don moriyar juna
2015-05-08 10:39:59 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwaransa na Kazakhstan Nursultan Nazarbayev sun amince su karfafa dangantakar manyan tsare-tsare da ke tsakaninsu don samun moriyar juna da kuma mutunta juna.

Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, kasashen biyu za su ci gaba da bunkasa hadin gwiwar da ke tsakaninsu a bangaren muhimman kayayyakin more rayuwa, makamashi, harkokin kudi, tsaro, al'adu, da kuma musaya tsakanin al'ummomin kasashensu.

Bugu da kari, shugaba Xi ya taya Nazarbayev murnar sake lashe zaben shugabancin kasar da aka yi a ranar 26 ga watan Afrilu. Kuma Sin na goyon bayan kokarin da Kazakhstan ke yi na neman karbar bakuncin bikin Expo na shekarar 2017, bikin da zai mayar da hankali kan taken "makomar makamashi"

A nasa jawabin, shugaba Nazarbayev ya ce, kasarsa na goyon baya kuma a shirya take ta shirin nan na gina zirin tattalin arziki na siliki da kuma shirin kasar Sin na gina al'umma mai makoma guda a yankin Asiya.

Ya kuma ce, kasarsa a shirye take ta yi aiki kafada da kafada da Sin karkashin shirin nan na CICA, da kuma bankin zuba jari kan ababan more rayuwa na Asiya (AIIB).

Bugu da kari shugabannin biyu sun tattauna kan batun kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da halin da ake ciki a tsakiyar Asiya da sauransu.

Wannan shi ne zangon shugaba Xi na farko a rangadin da yake karo na biyu a wannan shekara, ziyarar da ake fatan za ta kai shi kasashen Rasha da kuma Belarus. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China