Shugaban gidan rediyon kasar Sin CRI Wang Gengnian, ya sanya hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa, tare da shugaban jaridar Rossiyskaya Gazeta ta kasar Rasha Pavel Negoitsa, a fadar Kremlin dake kasar ta Rasha.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda ke ziyarar aiki a kasar Rasha, da kuma takwaransa na Rashan Vladimir Putin sun gane ma idonsu sanya hannu kan wannan yarjejeniya.
Rahotanni sun ce makasudin yarjejeniya shi ne kara inganta hadin gwiwa, a tsakanin kafofin yada labarai na kasashen biyu.
Da yake jawabi bayan bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar, shugaba Xi Jinping ya ce kasashen biyu za su gudanar da bikin karfafa mu'amala tsakanin kafofin yada labaransu, a shekarar 2016 da 2017.
Ana dai sa ran yarjejeniyar da aka daddale za ta taimaka ga inganta fahimtar juna, da dankon zumunci tsakanin jama'ar kasashen biyu, tare da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin kafofin yada labaran su. (Lubabatu)