A madadin gwamnati da jama'ar kasar Sin, shugaba Xi ya mika gaisuwa da fatan alheri ga gwamnati da jama'ar Rasha, inda ya bayyana cewa, bana ta cika shekaru 70 da cimma nasarar yakin duniya na biyu kumaSin da Rasha, muhimmin fagen yaki ne na Asiya da na Turai a yayin yakin duniya na biyu. A saboda da haka, bana kasashen biyu za su jagoranci jerin ayyukan murna da tunawa da wannan jarumtaka, domin bayyana niyyarsu ta tabbatar da sakamakon da aka samu bayan yakin duniya na biyu da kiyaye adalci a duniya tare. Ban da haka, Sin da Rasha, makwabtan juna ne kuma aminai wadanda suka kafa dangantakar abokantaka bisa manya tsare tsare a duk fannoni tsakaninsu, ta yadda suka zama abin koyi a fannonin kasancewa da juna cikin lumana da yin hadin gwiwa da samun moriyar juna.
Shugaba Xi ya sauka a birnin Moscow bayan da ya kammala ziyararsa a kasar Kazakhstan(Fatima)