in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan na goyon bayan Habasha game da ginin madatsar ruwa
2015-05-10 16:08:06 cri
Ministan albarkatun ruwa da wutar lantarki na kasar Sudan Mutaz Mussa, ya ce Habasha na da 'yancin gina babbar madatsar ruwan da take shirin farawa, domin amfana daga albarkatun kogin Nilu wanda ya ratsa kasashen yankin uku.

Mussa wanda ya bayyana hakan bayan ganawarsa da tawagar wakilan majalissar dokokin kasar ta Habasha dake ziyarar aiki a Sudan, ya kara da cewa hakkin Habasha ne, ta ci gajiyar albarkarun ruwa daga kogin na Nilu, muddin hakan ba zai shafi moriyar sauran kasashe masu ruwa da tsaki ba.

A cewarsa babbar madatsar ruwan da Habashan ke fatan ginawa, za ta zamo hanyar karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Sudan, da kuma Masar.

A watan Maris din da ya shude ne dai kasashen uku suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya, wadda ta shafi ginin wannan madatsar ruwa, da kuma hakkinsu na tarayya game da mallakar albarkatun kogin na Nilu.

Kasar Masar dai na nuna dari-darinta ga ginin wannan sabuwar madatsar ruwa, aikin da take kallo a matsayin abin da zai rage moriyarta game da kogin. Yayin da a daya hannun Habasha ke fatan aikin, zai ba ta damar fadada samar da wutar lantarki.

Madatsar ruwan dai za ta lashe kudi har dalar Amurka biliyan 4.7, za kuma a kammala gininta, nan da shekaru uku masu zuwa. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China