Wannan ne dai karo na 10 da tawagar ta gudanar da aikin samar da agajin jin kai a kasashen waje, wadda ta zama tawaga ta farko da ta sauka a kasar ta Nepal, bayan aukuwar bala'in girgizar kasar.
A ranar 25 ga watan Afrilun da ya shude ne dai girgizar kasa mai karfin digiri 8.1 bisa ma'aunin Richter a auku a kasar ta Nepal, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, yayin da wasu da yawa suka jikkata, baya ga hasarar dukiyoyi da ta haddasa. Jim kadan da abkuwar bala'in, gwamnatin Sin ta mai da hankali matuka kan wannan batu, inda ba tare da bata lokaci ba, ta tura tawagar aikin ceto zuwa kasar bisa bukatar mahukuntan ta.
Tawagar dai ta isa birnin Kathmandu da washegarin ranar da bala'in ya auku, ta kuma fara aikin ceto nan take. Baki daya dai ta ceto mutane 2, ta kuma tone buraguzan gine gine 430 a yankuna 18, tare da jiyyar mutane 2729, ta kuma fitar da kayayyaki sama da 910.
Da yake tsokaci game da wannan gudummawa, jakadan Nepal a nan kasar Sin Mahesh Kumar Maskey, ya jinjinawa gwamnatin ta Sin bisa tura tawagar ta zuwa Nepal, yana mai cewa kasar Sin aminiya ce ga Nepal. Kana kasashen biyu na fatan zurfafa dankon zumunci tsakaninsu, ta ayyukan farfado da kasar bayan bala'in girgizar kasar da ya auku. Bugu da kari a cewar jama'ar Nepal ba za su taba mantawa da taimakon da Sin ta bayaiwa Nepal ba. (Fatima)




