in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya ba da umurni game da aikin tunkarar bala'in girgizar kasa da ceton mutane a jihar Tibet
2015-05-07 10:30:21 cri
Kwanan baya ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sake ba da wani muhimmin umurni game da aikin yaki da girgizar kasa da ceton mutane a yankunan Shigatse da Ngari na jihar Tibet ta kasar Sin, inda ya amince da nasarar da aka samu a mataki na farko na aikin tunkarar bala'in da girgizar kasa ta haddasa da ceton mutane, amma ya bukaci a kara kokari, don ci gaba da nema tare da kubutar da mutane daga bala'in, da ba da aikin jinya ga wadanda suka ji rauni, da tsugunar da mutanen da bala'in ya rutsa da su. A sa'i daya kuma, ya bukaci a gaggauta gyara muhimman ababen more rayuwa da suka lalace, da gudanar da ayyukan sake farfado da dukkan abubuwan da suka lalace, don tabbatar da zaman lafiya da wadata a yankunan da bala'in ya shafa a jihar.

A ranar 25 ga watan Afrilu ne, bala'in girgizar kasa mai karfin maki 8.1 da wasu kanana da suka biyo baya, suka shafi yankunan Shigatse da Ngari na jihar Tibet, ya zuwa ranar 6 ga wata da karfe 5 na yamma, lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 26, tare da bacewar wasu 3, da jikkatar wasu sama da 850, baya ga mutane kimanin dubu 300 da ke fama da bala'in.

Bisa umurnin da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwa ta kasar suka bayar, an ce, ya zuwa yanzu, an tsugunar da mutane sama da dubu 63, an kuma dawo da hasken wutar lantarki da ruwa da harkokin sadarwa, tare da tabbatar da doka da oda a wurin.(Bako)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China