in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya sauka a birnin Astana na kasar Kazakhstan
2015-05-07 20:42:28 cri

A yammacin yau alhamis 7 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa Astana, babban birnin kasar Kazakhstan, zangon shi na farko a ziyarar da zai yi a kasashe uku a cikin kwanaki 6.

Wannan ne karo na biyu da shugaba Xi ya kai ziyara a kasar Kazakhstan bayan da ya hau kujerar shugaban kasar Sin. A watan Satumban shekarar 2013, shugaba Xi ya gabatar da shirin "hanya daya da ziri daya" karo na farko a yayin ziyararsa a Kazakhstan karo na farko, wanda ya samu karbuwa sosai daga kasashen dake dab da hanya da kuma zirin.

Bayan kammala ziyararsa a Kazakhstan, shugaba Xi zai wuce kasar Rasha, inda zai halarci bikin murnar cika shekaru 70 da samun nasarar yakin kiyaye kasar, daga nan kuma zai wuce kasar Belarus.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China