in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayern Munich ta lashe kofin Bundesliga a karo na 25 ba tare da wasu shagulgula ba
2015-05-05 11:10:32 cri
Sakamakon wasannin da ake bugawa a gasar Bundesliga ta kasar Jamus, ya nuna cewa yanzu haka kulaf din Bayern Munich ya kai ga matsayin lashe gasar ta bana, tum ma kafin a karasa ragowar wasanni da dama.

Duk da cewa lashe wannan kofi a karo na 25 babbar nasara ce ga Bayern Munich, a hannu guda rashin wannan dama na iya zama babbar asara ga kulaf din, kwanaki kadan da lashe kofin na bana, magoya baya, da kuma shi kan sa kulaf din basu gudanar da wani biki na nuna farin cikin su ba.

Wannan nasara dai ta tabbata ne, bayan da Bayern Munich din ta doke Hertha BSC da ci daya da nema, a wasan da suka buga ranar Asabar. Bayern Munich dai ta lashe wannan kofi a karon farko cikin shekara ta 1932.

An kuma tabbatar da nasarar Bayern din bayan kulaf din dake biye da ita a matsayi na biyu VfL Wolfsburg, ya rasa nasara a wasan sa da Borussia Moenchengladbach a ranar Asabar.

Ana dai danganta rashin fara bukukuwa a bangaren Bayern, da dakon manyan wasannin da ke gabanta, wato wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin zakarun turai, wanda za ta buga da Barcelona a ranekun 6, da kuma 12 ga watan Mayu mai zuwa.

Don haka a cewar kocin kulaf din Pep Guardiola, lokaci bai yi ba da zasu fara murna tunkuna. A ganin sa nasarar kulaf din za ta cika ne kadai, idan har suka dauki kofin zakarun turai dake daf da kammala.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China