in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Roberto Carlos ya ce babban burin sa shi ne ya zama mai horas da 'yan kwallon kasar Brazil
2015-04-16 15:19:03 cri

Tsohon shahararren dan wasan kasar Brazil Roberto Carlos, ya ce yana matukar burin kasancewa cokin kulaf din kasar Brazil a nan gaba.

Carlos dan shekaru 42 da haihuwa, wanda a yanzu haka ke horas da 'yan wasan kulaf din Akhisar, na kasar Turkiya, bayan ya bar kulaf din Sivasspor, ya ce ko shakka babu akwai babban aiki a gaban sa, amma duk da hakan ya na fatan cimma burin na sa komai dadewa.

Ya ce ya gamsu da rawar da ya taka lokacin da yake bugawa Brazil wasa tsahon shekaru 14, lokacin da kuma ya tallafawa kungiyar wajen lashe kofuna da dama, kamar kofin Copa America, da Confederations Cup, da kofin duniya. Wanda hakan ke sanya shi shaukin komawa gida ya kara bada wata gudummawar.

Carlos, wanda daya ne daga 'yan wasan Brazil lokacin da kasar ta dauki kofin duniya na shekarar 2002, ya kara da cewa ya na koyi da salon manyan koci-koci na duniya, kamar su Mario Zagallo, da Carlos Alberto Parreira, da Vicente del Bosque da kuma Luiz Felipe Scolari. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China