in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Uganda za ta karbi bakuncin gasar matasa ta 2015
2015-04-23 09:37:54 cri
Hukumar kwallon kafa ta kasar Uganda, ta ce Ugandan ce za ta karbi bakuncin gasar matasa 'yan kasa da shekaru 17 ta bana, gasar da za a gudanar cikin watan Disambar karshen shekara.

A cewar shugaban hukumar Moses Magogo, hukumar gudanar da kwallon kafa ta kasashen Gabashi da tsakiyar Afirka Cecafa ce ta amince da wannan mataki, yayin wani taro da ta gudana a birnin Nairobin kasar Kenya a juma'ar da ta gabata.

Da yake tabbatar da wannan batu, sakataren hukumar ta Cecafa Nicholas Musonye, ya ce an tattauna kan muhimman batutuwa a yayin taron jami'an hukumar, ciki hadda batun mika bakuncin wannan gasa ga kasar ta Uganda, da ma batun gasar Kagame da hukumar ke shiryawa.

Nicholas Musonye, ya kara da cewa gasar manyan kulaflika ajin kwararru ko "Challenge Cup" wadda ba a samu damar gudanarwa ba a bara, a yanzu za ta gudana a kasar Rwanda cikin watan Nuwamba, bayan kasar Tanzania ta karbi bakuncin gasar Kagame cikin watan Yuni.

Kasar Rwanda dai ta amince ta karbi bakuncin gasar Challenge Cup da Cecafa ke shiryawa, a shirye-shiryen ta na karbar bakuncin gasar nahiyar Afirka ta 2016.

Kasar Uganda ce dai ke rike da kofin Cecafa na matasa 'yan kasa da shekaru 17, bayan da ta samu nasarar doke Eritrea da ci 2 da nema a wasan karshe da suka buga a Sudan cikin shekarar 2009. Yayin da Kenya kuma ke rike da kofin ajin kwararru na champions Cup, bayan ta samu nasara kan Sudan a wasan karshe na shekarar 2013. Sai kuma kulaf din El Merreikh na kasar Sudan dake rike da kofin Kagame.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China