in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Man. United dake samun farfadowa sosai
2015-04-23 09:40:08 cri

Kwanakin baya, a wasan da ya gudana tsakanin manyan kuloflika 2 na birnin Manchester dake kasar Birtaniya, wato Man. United da Man. City, sun buga wasa a gasar Premier inda Man. United ta doke Man. City da ci 4 da 2, nasarar da ta kasance karo na 6 a jere da Man. United ta ci nasara a wasannin da suka buga karkashin tsarin gasar Premier.

Sai da wani abun mamaki shi ne bisa la'akari da yadda kungiyar ta taba kasancewa matsayi na 14 a teburin gasar ta Premier League mai kunshe da kwararrun kuloflikan kasar Birtaniya. Amma sannu a hankali cikin wasanni 13 da suka gabata, Man. United ta lashe abokan karawarta 9, ta kuma yi kunnen doki da wasu 2, inda ta samu maki 29, lamarin da ya sanya ta hawa matsayi na 3 a teburin gasar. Yanzu haka dai gibin dake tsakanin Man. United da kungiyar Arsenal dake matsayi na 2 maki 1 ne kacal.

Hakika Man. United a yanzu ba wai kungiya ce maras karfi ba tun a farkon kakar wasan da ake ciki, musamman ma bisa la'akari da yadda kungiyar take gwada karfinta a karawarta da sauran manyan kulflika. Ga misali ta lashe Liverpool a wasanni 2 da suka halarta da ci 3 da nema, da ci 2 da 1. Sa'an nan ta lashe Man. City da ci 4 da 2 kamar yadda muka ambata. Haka kuma ta lashe Arsenal da ci 2 da 1.

Bisa wadannan nasarori da ta samu, za a iya ganin cewa kungiyar Man. United a karkashin jagorancin kocinta na yanzu Louis van Gaal, ta fi karfi fiye da yadda take karkashin kulawar tsohon kocin ta David William Moyes.

Wani abin da ya sa ake ganin kwarewar Louis van Gaal shi ne, yadda ya sa wasu 'yan wasa, wadanda ba su samar da wata babbar gudummawa ga kungiyar a lokacin da David Moyes yake kulawa da kungiyar Man. United, a yanzu suka fara shaida karfinsu.

Ga misali Ashley Young, wanda ke cikin jerin sunayen 'yan wasan da ake son sayarwa wasu kuloflika a lokacin zafi da ya wuce, yanzu haka ya na shaida kwarewarsa matuka a wasan da aka buga da kungiyar Man. City, inda ya zura kwallo bisa nuna kwarewa matuka a wasan su na baya baya da Man. City. Haka Young sau biyu yana mika kwallo daga gefen hagu, wanda hakan ya baiwa kungiyar damar cin karin kwallaye.

A nasa bangaren, Marouane Fellaini shi ma ya fara nuna alamu na kwarin gwiwa, ganin yadda wannan dan wasa mai tsayi da karfi ya kasa samun ko da kwallo daya a kakar wasanni da ta wuce, amma a wanna kaka yanzu haka ya riga ya zura kwallaye 5 cikin raga. Fellaini ya samu wannan ci gaba ne bisa yadda babban kocin kungiyar Louis van Gaal ya canza matsayinsa. A da Fellaini yana zaune ne a tebur, amma yanzu van Gaal ya tura shi gaba, inda yake amfani da tsayin sa wajen taro kwallon sama.

Alkaluma sun nuna cewa a wasan da Man. United ta kara da Man. City, Fellaini ya yi amfani da tsayin sa wajen taro kwallo har karo 11, inda ya samu nasarar tare kwallaye 9. Sa'an nan duk lokacin da ya samu kwallo, hakan na zama dama ga kungiyar Man. United, don ta fara tasam ma ragar abokan karawarta. Fellaini ya kan mika kwallo ga Ashley Young, ko kuma Daley Blind, wadanda suke jagorantar kai hari ga abokan karawar su.

Idan mun dubi cikakken tsarin wasa da shi Van Gaal yake dauka, za mu ga babban sauyi da aka samu, idan an kwatanta da na tsohon tsarin wasa kocin Moyes. A takaice dai, Van Gaal ya fi mai da hankali kan gefuna 2 maimakon tsakiyar fili, a yayin da ake kokarin neman cin kwallo.

Ga misali, a wasan da aka buga tsakanin Man. United da Man. City, Van Gaal ya sanya Daley Blind, da Ashley Young, da Fellaini a gefen hannun hagu, sa'an nan a hannun dama yana da Luis Antonio Valencia, da Juan Mata, da Ander Herrera, inda shi Mata ke iya kula da tsakiyar fili, bisa kwarewarsa a fannin gudu cikin sauri.

Sakamakon da aka samu a wasannin da Man. United ta buga ya shaida cewa, matakan da Van Gaal ya dauka daidai ne. Yanzu haka dai karfin kungiyar Man. United a bangaren samun nasara yayin mika kwallo ya kai kashi 82%. Hakan ya sa 'yan wasan kungiyar suke iya mika kwallo tsakanin junan su, ba tare da tsoron ganin an kwace kwallon ba, wanda hakan ke bada zarafin zura kwallo cikin raga.

Ganin ci gaban kungiyar Man. United ya sa ake kwatanta Van Gaal da tsohon kocin kungiyar Alex Ferguson, domin dukkansu na da fasahar daidaita tsarin wasan kungiyar, wajen sanya dukkan 'yan wasan nuna kwarewar su sosai. Yadda kungiyar ta kasa taka rawar gani a karkashin jagorancin Moyes, da yadda a yanzu take samun farfadowa, da sake nuna karfi a karkashin kulawar Van Gaal, ya shaida cewa baya ga samun kwararrun 'yan wasa, abin da ya fi muhimmanci shi ne dabarar da kocin wata kungiyar yake dauka.

Idan koci bai san fasahar yin amfani da 'yan wasa yadda ya kamata ba, to, da wuya kungiyar sa ta iya taka rawar a-zo-a-gani. Amma idan koci ya san hanyar da zai bi wajen sanya 'yan wasansa nuna kwarewarsu, to ko da 'yan wasa masu rangwamen kwarewa, zai iya kaiwa ga cimma nasara.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China