Adjei ya samu nasarar cin kwallaye 16, a gasar da ta gudana a kasar Seychelles, an kuma zabe shi a matsayin gwarzon dan wasan ne, bayan da ya buga wa kasar sa wasanni 4, duk kuwa da cewa kulaf din da yake wakilta wato Black Sharks na kasar Ghana, bai samu nasarar lashe gasar ta wannan karo ba.
Wannan ne dai karon farko da kungiyar ta Black Sharks ta samu zarafin shiga wannan gasa, inda ta zamo a matsayi na 7, yayin da sauran kasashen Afirka 8 suka fafata a gasar.
Da yake tsokaci game da nasarar da dan wasan kulaf din sa ya samu, cokin kasar ta Ghana Daniel Kotey, ya ce sun koyi darussa da dama a gasar ta Seychelles, irin darussan da za su basu damar karfafa kwarewar su a nan gaba.
Kasar Madagascar ce dai ta lashe kofin na bana, bayan da ta ci dukkanin wasannin da ta buga a gasar. Yanzu haka kuma Madagascar da kasar Senegal ne za su wakilci nahiyar Afirka, a gasar kwallon rairayi ta duniya wadda hukumar FIFA za ta shirya a kasar Portugal.