Halin da ake ciki na sauyawa yadda ake so domin sojojin Nijar sun shiga fagen daga a cikin Najeriya, in ji ministan Nijar a yayin wata tattaunawa tare da shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara.
A cewarsa, tawagar sojojin Nijar ta shiga sosai cikin aiwatar da matakin da aka dauka bisa tsarin kwamitin kasashen dake kewayen tafkin Chadi.
Mista Mohamed Bazoum ya jaddada wajabcin sanar da shugaba Ouattara kan halin da ake ciki game da matsalar tsaro a cikin shiyyar, bisa ga rawar da yake takawa a yammacin Afrika.
"Fatanmu shi ne na ganin wannan yaki ya kare bisa nasarar da gamayyar kasa da kasa ke fatan a samu", in ji mista Bazoum tare da kara bayyana jin dadinsa kan kokarin da ake na hadin gwiwa domin yaki da kungiyar Boko Haram ta Najeriya dake barazanar hargitsa Najeriya da makwabtanta.
Rundunar sojojin Najeriya, tare da taimakon sojojin kasashen Kamaru, Chadi da Nijar dake makwabtaka da Najeriya, sun kaddamar da samame tare da samun nasarar kwato wasu yankuna daga hannun Boko Haram a arewa maso gabashin kasar. (Maman Ada)