Bayanin ya nuna cewa ya zuwa daren jiya, girgizar kasar mai karfin digiri 5.8 da 5.9 bisa ma'aunin Richter, ta shafi mutane dubu 14 a birnin biranen Puer da Lincang, yayin da wani mutum guda ya rasa ransa, baya ga wasu mutanen 15 da suka jikkata.
Kaza lika kididdiga ta nuna cewa dakuna 36 na gidaje iyalai 12 sun rubta, yayin da wasu dakunan 1033 na gidaje iyalai 224 334 suka yi matukar lalacewa. Sai kuma wasu dakunan 2411 na gidaje iyalai 804 da suka dan tabu. A kuma halin yanzu ana ci gaba da nazari kan halin da ake ciki a yankunan da wannan annoba bala'in ta ya aukawa.
Wakilinmu ya ce ya yin taron manema labaru da hukumar lura da girgizar kasa ta lardin Yunnan din ta gudanar da misalin karfe 9 na daren jiya, dukkanin bala'un biyu, tasiri ne na girgizar kasar da ta abku a ranar 7 ga watan Okbota, wadda karfin ta ya kai digiri 6.6 bisa ma'aunin Richter. A wannan karo dai, ba ya ga jikkatar mutane, girgizar kasar ta haifar da lalacewar manyan ababen more rayuwa, kamar hanyoyi, da bututun samar da ruwan sha da dai sauransu.(Fatima)