Bisa labarin da ofishin watsa labaru na birnin Lincang na lardin Yunnan na kasar Sin ya bayar, an ce, ya zuwa karfe 9 na daren ranar 1 ga wata, mutane 67039 ke fama da bala'in girgizar kasa mai karfin maki 5.5 bisa ma'aunin Richter da ta abku a garin Cangyuan na birnin, wanda kuma jikkata mutane 32, a yanzu haka bangarori daban daban na gudanar da aikin ba da ceton gaggawa yadda ya kamata, kuma an tsugunar da mutane 12374 dake fama da bala'in.
Girgizar kasar mai karfin maki 5.5 bisa ma'aunin Richter ta afkawa garin Cangyuan na birnin Lincang ne a ranar 1 ga wata da karfe 6 da minti 24 na yamma.
A halin yanzu, jami'an birnin da na gari da sojoji da 'yan sanda da sojojin kota kwana da yawansu ya kai kimanin dubu daya na cigaba da gudanar da ayyukan ceto a yankin mai fama da bala'in. (Zainab)