Wanann shi ne karo na farko da kasar Sin ta tura bataliyar sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa kasashen ketare domin gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa, kuma bisa umurnin da aka bayar, da farko sojojin guda 180 na balaliyar za su tafi kasar Sudan ta Kudu ta jigaren sama dauke da kayayyakin da ake bukata na yau da kullum a farkon watan Janairu na shekarar 2015, daga baya wasu sojojin za su isa kasar a watan Maris na shekarar 2015 ta jiragen sama ko na ruwa.
Bataliyar mai sojoji guda 700 sun hada da jami'an soja guda 121, yayin da sojoji guda 579.
A watan Yuli na wannan shekarar ce, MDD ta gayyaci kasar Sin da ta kafa wata bataliyar sojojin kasa ta kiyaye zaman lafiya a hukunce, domin gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya bisa bukatun tawagar musamman ta MDD dake kasar Sudan ta Kudu.
Kafin wannan kuma, dukkanin rundunonin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin galibi rundunoni ne da ke kunshe da magina, aikin sufuri, aikin likitanci da kuma 'yan sanda. Lamarin da ya nuna cewa, wannan shi ne karo na farko da kasar Sin ta tura bataliyar sojojin kiyaye zaman lafiya a tarihin aikin kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ke shiga. (Maryam)