Yu ya bayyana hakan ne yau a nan birnin Beijing lokacin da yake ganawa da tawagar jam'iyyar NCP mai mulki a Sudan karkashin jagorancin mataimakin shugaban jam'iyyar kana mataimakin shugaban kasar Sudan Ibrahim Ghandour.
Mr Yu ya ce, a ko da yaushe JKS da gwamnatin kasar Sin suna daukar dangankatar kasashen biyu da muhimmancin gaske. Sannan kasar Sin za ta ci gaba da nuna gaskiya tare da kokarin kare moriyarsu yayin da take bunkasa dangantaka da kasashen Afirka.
A nasa jawabin Ibrahim Ghandour ya ce, Sin sahihiyar abokiyar Sudan ce, kuma yana fatan kasarsa za ta yi koyi da nasarorin da Sin ta samu yayin da take kara zurfafa musaya tsakanin kasashen da kuma jam'iyyunsu da ke mulki. (Ibrahim Yaya)