Rahotanni dai sun tabbatar da cewa wannan layin dogo da aka gina a yankunan tuddan kasar Sin, su ne irin su na farko a dukkanin fadin duniya. Yanzu haka dai lardunan Gansu, da Qinghai, da jihar Xinjiang sun shiga jerin yankunan kasar Sin dake amfani da jiragen kasa mafiya sauri.
Kaza lika bude wadannan hanyoyi na jiragen kasa mafiya sauri tsakanin birnin Lanzhou da jihar Xinjiang, ya kawo karshen rashin sifirin jiragen kasa tsakanin biranen Urumqi da Xi'ning.
An ce, tsawon hanyoyin jiragen kasan mafiya sauri tsakanin Lanzhou da jihar Xinjiang, ya kai kilomita 1776, an kuma fara ginin su ne a watan Janairun shekarar 2010. (Zainab)