Budewar wannan hanyar jiragen kasa ta samar da sauki ga jama'ar yankin Tibet ziyartar iyalan su da kuma yin addu'a, kana ta samar da sauki ga mutanen da suka zo yankin Tibet don yawon shakatawa.
Shugaban kamfanin jirgin kasa mai samfurin Z8801 dake tashi daga Lhasa zuwa Shigatse Wang Lei ya bayyana cewa, wannan jirgin kasa ya iya tashi zuwa Shigatse da komawa Lhasa a cikin yini daya, wanda ya samar da sauki ga masu yawon shakatawa da 'yan kasuwa na wuraren biyu.
Hanyar jiragen kasa a tsakanin Lhasa da Shigatse da aka gina a shekarar 2010 ta kasance kari ne na farko a kan layin dogo na jiragen kasa a tsakanin Qinghai da yankin Tibet a kasar Sin, wadda aka zuba jari da kudin Sin Yuan biliyan 13.28, saurin jiragen kasa a kan layin bai yi kasa da kilomita 120 a kowace awa ba. Wannan hanya ta bude sabon shafi na tarihin doguwar hanyar motoci daya kawai a yankin kudu maso yammacin yankin Tibet. (Zainab)