Wata kididdiga da aka fitar ta nuna cewa a bara, an gudanar da ayyukan shimfida hanyoyin jiragen kasa na cikin birane 36 dake nan kasar Sin, wadanda tsawonsu ya kai kilomita 3300, kuma wannan aiki ya lashe kudin Sin RMB Yuan biliyan 285.7, wato kimanin Yuan miliyan 780 a kowace rana ke nan. Adadin da ya karu da kashi 33 bisa dari idan an kwatanta shi da na shekarar 2013.
Aikin shimfida hanyoyin jiragen kasa na cikin biranen kasar Sin dai shi ne na uku, inda yake biye da na shimfida manyan hanyoyin mota, da na jiragen kasa masu tafiya nesa a fannin yawan zuba jari.
An bayyana hakan ne dai yayin bikin nune-nune na hanyoyin jiragen kasa na kasar Sin na bana, wanda aka bude yau Laraba a birnin Shanghai.
Bisa kididdigar da kwamitin bunkasa kasa da gudanar da gyare-gyare na kasar Sin ya gabatar, an ce, ya zuwa karshen shekarar 2014, biranen kasar 22 sun gina layin dogo na birane har 101, wadanda tsawonsu ya kai kilomita 3155. (Lami)