Yawan jarin da aka zuba a fannin shimfida layin dogo a kasar Sin a bara ya kai matsayin koli a tarihi
Kasar Sin ta gabatar da wasu matakan gaggauta bunkasa harkar sufurin jiragen kasa a shekarar 2014 da ta gabata, inda yawan jarin da aka zuba a fannin sufurin jiragen kasa a kasar ya kai kimanin kudin Sin Yuan biliyan 800, kana tsawon sabon layin dogo da aka gina ya zarce kilomita 8000, yayin da jarin da aka zuba da ayyukan ginin layin dogo a shekarar ta 2014 ya kai matsayin koli a tarihi.
A shekarar 2014, kasar Sin ta maida hankali kan gaggauta bunkasa layin dogo, musamman ma fannin gina sabbin layin dogo a tsakiya da yammacin kasar Sin. Inda babban kamfanin sufurin jiragen kasa na kasar Sin ya gudanar da ayyuka a matakin farko, don tabbatar da nasarar gina sabbin layin dogon a kan lokaci.
Ya zuwa karshen shekarar ta bara, an riga an amince da ayyuka 64, an kuma fara gudanar da dukkanin su a halin yanzu. (Zainab)