Mr. Hong, wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labaru a Jumma'ar nan, ya kara da cewa Sin za ta ba da dukkanin gudummawa, domin cimma nasarar da aka sanya gaba, a zagayen shawarwarin da za a gudanar a ranekun 22 da 23 ga watan nan a birnin Vienna.
A ranar 2 ga watan nan ne dai kasashe 6 da batun nukiliyar Iran ya shafa da ita kanta Iran din, suka cimma matsaya game da matakan da za a dauka a yayin shawarwarin da za a gudanar na gaba, shawarwarin da ake fatan za su ba da damar kaiwa ga cimma matsaya, nan da ranar 30 ga watan Yuni mai zuwa.
Mr. Hong ya kara da cewa daga yanzu zuwa wannan wa'adi, za a gudanar da tattaunawa kan muhimman batutuwa, don haka Sin ke fatan dukkanin sassan da wannan batu ya shafa za su dauki matakan da suka dace, domin samun nasarar shawarwarin.
Tuni dai aka sanar da cewa wakilai a fannin siyasa na kasashen da wannan batu ya shafa, za su gudanar da taruka na kwanaki biyu, a wani mataki na kokarin cimma matsaya guda. (Saminu Hassan)