Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan cikin sakon da ya aiko daga kasar Fiji da a halin yanzu ke ziyarar aiki ya ce, wajibi ne hukumomin lardin Sichuan da na jin dadin jama'a su shirya ayyukan ceto yadda ya kamata kana su yi iyakacin kokarinsu don rage yawan asara.
Wata tawagar masu aikin ceto mai wakilai 35 ta iasa garin Tagong kimanin sa'o'i biyu bayan aukuwar girgizar kasar. Bugu da kari akwai jiragen soja, ma'aikatan lafiya 60 da kimanin sojoji 1,000 da ke zaman shirin ko ta kwana.
Shi ma firaministan kasar Sin Li Keqiang ya ba da umarnin tantance barnar da girgizar kasar ta haifar sannan ya bukaci hukumomin tunkarar bala'u da su aike da tawagogin aikin ceto don ba da jagoranci ga aikin ceton da ake a wurin.
Yanzu dai sashen kula da girgizar kasa na majalisar gudanarwar kasar Sin da sashen kula da girgizar kasa na lardin Sichuan sun kaddamar da aikin kota kwana tare da aikewa da tawagogin aikin ceto zuwa garin kangding. An kuma aike da kayayyakin samar da wuta, tantuna da tabarmai zuwa wuraren da girgizar kasar ta shafa.
A jiya da yamma ne da misalin karfe 4.55 agogon kasar Sin wata girgizar kasa mai karfin maki 6.3 ta fadawa yankin Garze da ke lardin Sichuan, inda kimanin mutane 4 suka mutu, 54 suka jikkata baya ga mutane 79,500 da bala'in ya shafa.(Ibrahim)