in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 5 sun mutu a sakamakon girgizar kasa da ta faru a gundumar Kangding dake yammacin kasar Sin
2014-11-24 16:08:39 cri
Ya zuwa karfe 8 na daren ranar 23 ga wata, bisa agogon wurin, mutane 5 sun mutu a sakamakon girgizar kasa da ta abku a gundumar Kangding na lardin Sichuan a ranar 22 ga wata, kuma mutane 54 sun ji rauni. Girgizar kasar tana shafar gundumomi 6 da kauyuka 55 gami da ritsar da mutane dubu 79. A halin yanzu, ana gudanar da ayyukan ceton mutane yadda ya kamata.

Cibiyar bada jagoranci ga aikin ceto da aka kafa a kauyen Duola na gundumar Kangding wanda ya fi fama da bala'in, ta fara gudanar da ayyukanta, kuma aka kai tantuna da barguna da tufafi zuwa yankin, da samu siginar wayar salula yadda ya kamata, gami da tabbatar da samar da wutar lantarki.

A halin yanzu, yawan rukunonin likitoci da suka isa yankuna masu fama da bala'in ya kai 11, kuma yawan likitocin da suka shiga aikin bada jinya ya kai 886, yayin da yawan ma'aikatan rigakafi da cututtuka masu yaduwa da kiwon lafiya da suka fara gudanar da aiki a wurin ya kai 104. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China