An ba da labarin cewa, mutum daya ne ya rasa ransa, sannan wadansu 324 suka jikkata sakamakon girgizar kasa mai zurfin maki 6.6 da ya afka a jihar Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin a daren Talatan nan.
Kamar yadda bayani ya nuna, wadanda suka ji rauni galibin su daga yankin Jinggu ne inda a nan ne ake lura da girgizar kasar. Gaba daya dai mutane 92,700 wannan bala'i ya shafa, sannan 56,880 daga cikin, an riga an samo musu matsuguni, inji wani jami'i na bangaren watsa labarai na wannan yankin.
Girgizar kasar dai ta abku ne da misalin karfe 9 da minti 49 na dare, agogon Beijing, sannan zurfin shi ya kai kilomita biyar, abin da ya girgizar yankin mai mutane 290,000.
An ji karfin girgizar a daukacin jihar Yunnan, wadda daman take yawan fuskantar bala'u daga indallahi.
Gwamnatin Yunnan ta kafa shirin ba da taimakon gaggawa mataki na farko wanda nan take aka aika da ma'aikatan ba da agaji na gaggawa tare da kayayyakin aiki.
A ranar 3 ga watan Agusta ma girgizar kasar mai zurfin maki 6.5 ta afka a yankin Ludian na jihar Yunnan, abin da ya yi sanadiyar mutuwar fiye da mutane 600. (Fatimah)