in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba za a ratsa kasar Chile a gasar Rally Dakar ta 2016 ba
2015-04-16 15:07:59 cri
Ministan wasanni na kasar Chile Natalia Riffo, ya ce a sakamakon bala'in ambaliyar ruwa da ya aukawa arewacin kasar ta Chile, ba za a ratsa kasar a gasar tseren motoci ta Dakar ta shekarar 2016 ba.

Riffo ya bayyanawa wani taron manema labaru cewa, a halin yanzu, hanyoyin motoci a yankin arewacin kasar Chile sun lalace a sakamakon bala'in, musamman hanyoyin motoci dake birnin Copiapo dake yankin Atacama, don haka ba bu tabbacin karbar bakuncin gudanar gasar tseren motoci ta Dakar a wannan yanki na kasar a shekarar dake tafe.

A 'yan kwanakin baya ne bala'in ambaliyar ruwa ya aukawa manyan yankuna 3 dake arewacin kasar Chile, wanda ya yi matukar lalata gine-gine, da hanyoyin motoci, da gadoji da sauran ayyukan more rayuwa. Har wa yau mutane 26 sun rasa rayukan su sakamakon bala'in, yayin da kuma mutane 125 suka bace. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China