in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar wasan kwallon kafar Ingila ta gabatar da shirin gyare-gyare
2015-04-01 16:03:24 cri

Babbar hukumar gudanarwar wasan kwallon kafar Ingila, ta fidda wani sabon shiri na gyare-gyare a 'yan kwanakin baya, wanda ke kunshe da wasu sabbin manufofi, da za su rage yawan 'yan wasa daga kasashen Turai buga kwallon kafa a kulaflikan kasar ta Birtaniya, a wani mataki na tallafawa horar da 'yan wasan 'yan asalin kasar Birtaniyan.

Bisa wannan shirin da za a fara gudanar da shi a watan Mayu mai zuwa, idan wani dan wasa wanda ba dan asalin daya daga kungiyar kasashen Turai EU ba ne yana so ya buga kwallon kafa a kasar Birtaniya, to, tilas kungiyar kwallon kafar kasarsa ta zama cikin kungiyoyi mafiya karfi 50 a duniya, bisa jadawalin da hukumar wasan kwallon kafa ta duniya FIFA ta jera sunayen kungiyoyin kasashen daki daki.

Wannan ka'ida dai za ta kasance mai tsanani bisa la'akari da yadda a da, ake bukatar dan wasa ya kasance cikin daya daga kungiyoyi mafiya karfi 70. Wato dai ana iya cewa an daga matsayin da ake bukatar dan wasa ya cika kafin ya samu damar taka keda a kasar Birtaniya ke nan.

Bisa sabon jerin sunayen kungiyoyin kasashe daban daban da hukumar FIFA ta gabatar, kungiyar kasar Sin ta kasance ta 83, saboda haka dukkan 'yan wasan kwallon kafar kasar Sin, ba su da damar neman buga kwallo a Birtaniya.

Hakika ban da 'yan wasan kasar Sin, 'yan wasa da dama na sauran wasu kasashen masu kwarewa a fannin buga kwallon kafa, kamar su Japan dake matsayi na 53, da Koriya ta Kudu wadda ke matsayi na 56, da kasar Australiya dake matsayi na 65, dukkansu ba za su samu damar buga kwallon kafa a wani kulob din Ingila ba. Ko da yake wannan mataki da za a dauka ba zai shafi kasashen dake yammacin Afirka sosai ba, ganin yadda kasashen suke kan gaba a duniya a fannin wasan kwallon kafa.

Bisa jerin sunayen da hukumar FIFA ta sanar, an ce kasar Cote d'Iviore tana kan matsayi na 20, yayin da Ghana ita ce ta 24, sa'an nan Najeriya tana matsayi na 41.

Sai dai kuma ko da kungiyar kasar da dan wasan yake, tana cikin kungiyoyi 50 mafi karfi a duniya, a daya hannun karkashin wancan shiri na hukumar wasan kwallon kafar Ingila, akwai wasu karin sharuddan da za a cimma kafin a ba su izinin shiga kasar Birtaniya.

Ga misali, idan shekarun dan wasa suka wuce 21, za a duba yawan wasannin da ya buga a kungiyar kasarsa a tsawon watanni 24 da suka gabata. Sa'an nan game da 'yan kasa da shekaru 21, za a tantance yawan wasannin da suka buga cikin kungiyar kasar su a tsawon watanni 12 da suka gabata.

Wato za a binciki tsawon lokacin da dan wasa ya kwashe ya na taka leda a matsayin dan wasan gida kenan. Haka zalika, akwai bambanci tsakanin tsawon lokacin da ake bukata bisa matsayin kungiyar kasar da dan wasan ya fito. Ga misali, idan kungiyar dan wasan tana cikin kungiyoyi 10 mafi karfi a duniya, ana bukatar cewa dan wasan ya halarci kashi 30% na dukkan wasannin kasa da kasa da kungiyar ta sa ta buga. Sa'an nan idan kungiyar tana tsakanin masayi na 11 zuwa 20, za a bukaci dan wasan da ya halarci kashi 45% na yawan wasannin da kungiyarsa ta buga.

Baya ga haka, sai kungiyar dake tsakanin ta 21 zuwa ta 30, inda ake bukatar dan wasan dake neman izinin shiga kasar Birtaniya, da ya buga kashi 60% na wasannin da kungiyar sa ta halarta. Sai dan wasan dake buga wa wata kungiya dake tsakanin matsayin 31 da 50, wanda ya kamata ya shaida kwarewar sa a kashi 75% na dukkan wasannin da kungiyarsa ta buga.

A cewar shugaban hukumar wasan kwallon kafar ta Ingila, mista Greg Dyke, sabbin manufofin da za a fara gudanarwa za su sanya 'yan wasa 42, daga cikin 'yan wasa baki 129 dake taka leda a kulofulika 92 na Ingila, rasa samun damar sabunta wa'adin su na visa.

Mista Dyke ya ce, kashi 55% na 'yan wasa baki dake buga kwallo a gasar Premier, wato tsarin gasar fitattun kulofulika na kasar Birtaniya, ba su nuna kwarewa sosai ba, domin lokacin da suka kwashe su na halartar wasanni a gida ya yi kasa da matsakaicin lokacin da ake bukata. Haka kuma, a kakar wasa ta 2 bayan da 'yan wasan suka fara taka kela a karkashin Premier League, kashi 42% daga cikin su, su na sauya sheka, ko kuma sauka zuwa tsarin gasar 'yan wasan da ba su da kwarewa sosai.

Hakan ya nuna cewa, wadannan 'yan wasa ba sa nuna kwarewa sosai, yayin da suke taka leda a karkashin tsarin Premier League na kasar Birtaniyan.

Bisa hakan ne kuma mista Dyke ya gabatar da shirin gyare-gyare, inda ya ce, sabbin manufofin da za a dauka za su sanya a gano 'yan wasan kwallon kafa mafiya kwarewa na kasashe daban daban, gami da kara samun damar janyo su zuwa kasar Birtaniya. An ce, sabon tsarin da za a dauka na kunshe da wasu ka'idoji masu tsanani, don haka 'yan wasan da ba su cimma matsayin da ake bukatar ba, da wuya su samu damar taka leda a kasar Birtaniya a nan gaba.

Ban da haka kuma, sabbin ka'idojin da za a dauka sun kayyade cewa, ya kamata kulofikan gasar Premier League su kara daukar 'yan wasan 'yan asalin kasar Birtaniya. An ce, ya kamata a tabbatar da yawan 'yan wasa 'yan asalin Birtaniya a kalla 12 cikin 25 da suke taka leda a jerin farko, cikin ko wane kulob din Premier League tsakanin shekarar 2016 da ta 2020, maimakon 'yan wasa 8 da aka kayyade a yanzu,. Haka zalika, an nanata cewa, dan wasan da ya halarci wani kulob din kasar Birtaniya kafin shekarunsa su kai 15 ne ake ganinsa a matsayin dan wasan dan asalin kasar, yayin da shekarun da aka kayyade a baya ke 18.

Hakika an dauki wannan mataki ne domin kyautata yanayin tsarin gasar Premier League, gasar da ta fi kunsar kuloflika da 'yan wasa kwararru, sai dai ba a samun 'yan Birtaniya masu yawa a cikinta. Ga misali, cikin kungiyoyi 32 da suka halarci gasar cin kofin zakarun kulflikan nahiyar Turai na bana, 'yan wasan Birtaniya 23 ne kawai, yayin da 'yan Spainiya su ka kai 78, haka kuma 'yan kasar Jamus sun kai 55, 'yan kasar Brazil su 51. Sa'an nan bayan da aka kammala wasan zagayen kungiyoyi 16 na wannan gasar, an fid da dukkan kungiyoyi 4 na kasar Birtaniya, abun da ya karfafa niyyar hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Birtaniya wajen gudanar da wadannan gyare-gyare.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China