in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kara tallafawa MDD a kokarin gudanar da aikinta
2014-10-08 10:59:27 cri
Zaunannen wakilin kasar Sin da ke MDD, mista Liu Jieyi, ya furta a ranar talata 7 ga wata cewa, MDD ta cimma nasarori a fannoni daban daban a shekarar da ta wuce, don haka a nata bangare kasar Sin na son hada kai tare da sauran mambobin majalisar don kara tallafa ma kokarin ta na gudanar da aikinta.

Mista Liu ya yi furucin ne a wajen wani zama karkashin inuwar babban taron MDD karo na 69 wanda aka kira domin sauraron rahoton da babban magatakardar majalisar ya gabatar dangane da aikin majalisarsa. Mr Liu ya ce a shekarar da ta gabata, MDD ta ci gaba da kokarin sa kaimi ga bangarori daban daban domin ganin sun yi hadin gwiwa, kana ta dauki jerin matakai don neman kwantar da kurar da ta tashi a yankuna daban daban. Haka zalika majalisar ta tsara shirin raya kasa na bayan shekarar 2015 don raya tattalin arziki da zaman al'umma na kasashe daban daban. Ban da haka kuma ta samu nasarori da yawa a fannonin aikin jin kai, kwance damara, yaki da ta'addanci, da dai makamantansu. Ta haka majalisar ta mayar da martani ga bukatun mambobinta, tare da karfafa matsayin kanta a wani tsari na duniya da ya kunshi bangarori da yawa. Bisa wannan sakamako ne in ji shi kasar Sin ta yaba ma babban magatakardan majalisar da sakateriya mai kula da aikin MDD kan kokarin su na sauke nauyin dake bisa wuyansu.

Haka zalika, a yayin da ya tabo maganar wasu batutuwan dake janyo hankalin jama'ar kasashe daban daban, mista Liu ya ce, kasar Sin tana goyon bayan kasar Iraki kan kokarinta na neman samun 'yancin kai da mulkin kanta, gami da cikakkiyar harabarta. Kana a cewar mista Liu, Sin tana fatan ganin bangarorin kasar Syria za su tsagaita bude wuta, da fara yin shawarwari cikin lokaci. Sai dai kuma kasar Sin ba ta amince da duk wani nau'in aikin ta'addanci ba, don haka kasar take goyon bayan gamayyar kasa da kasa don su daidaita matsayinsu a kokarin dakile 'yan ta'adda, bisa kudurin kwamitin sulhu na MDD. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China