in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya gana da babban sakataren MDD
2014-09-28 16:03:00 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin mista Wang Yi ya gana da babban sakataren MDD Ban Ki-moon a bakin babban taron MDD da ya halarta a jiya 27 ga wata, inda jami'an 2 suka yi musayar ra'ayi kan wasu batutuwan da suka shafi MDD tare da cimma matsaya sosai.

Wang Yi ya ce, dakile ta'addanci ya zame wa gamayyar kasa da kasa wani aiki dake bukatar kulawa cikin gaggawa, sai dai kafin a dauki wani mataki na soja ya kamata a samu izini daga wajen kwamitin sulhu na MDD.

Dangane da kwaskwarimar da ake shirin yi wa MDD, ministan kasar Sin ya ce, yayin da ake gudanar da wannan aiki ya kamata a lura da fannoni daban daban, kana a mai da kiyaye halaltaccen hakki na kasashe masu tasowa wani babban burin da ake neman cimmwa.

Ministan ya kara da cewa, neman samun ci gaba wata hanya ce da za a iya binta domin daidaita matsalolin da kasashen duniya suke fuskanta, don haka aiki na tsara shirin raya kasa bayan shekarar 2015 zai zama wani aiki mai muhimmancin gaske da MDD za ta kula da shi a shekara mai zuwa.

A nasa bangaren, mista Ban Ki-moon ya ce, kasar Sin a kullum tana baiwa MDD goyon baya sosai, kana ta samar da babbar gudunmowa ga kokarin majalisar na wanzar da zaman lafiya. Har wa yau kuma, kasar Sin ta zama abin koyi a fannonin tinkarar annobar Ebola da ba da tallafin jin kai, abin da ya kara yaukaka dangantakar dake tsakanin MDD da kasar Sin. A cewar mista Ban, a halin yanzu ana ci gaba da fama da wasu matsaloli a kokarin neman ci gaban duniya, saboda haka majalisarsa na fatan ganin kasar Sin za ta ci gaba da ba ta goyon baya a kokarin da ake yi na tsara shirin neman ci gaba a bayan shekarar 2015, tare da aiwatar da shi yadda ya kamata. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China