in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Saudiyya ta sanar da dakatar da kai farmaki ta sama a kasar Yemen
2015-04-22 10:01:40 cri

Wani jami'in rundunar sojojin kasar Yemen ya ce jiragen saman soja na kasar Saudiyya, da ma sauran kasashe masu mara mata baya, sun kaddamar da farmaki ta sama a wasu yankuna na jihar Ibb dake kudancin kasar Yemen a jiya Talata, matakin da ya haddasa kisan fararen hula 24.

A kuma dai jiyan ne kasar Saudiyya ta yanke shawarar dakatar da kai hare-hare ta sama karkashin shirin da aka yi wa lakabi da "Tsattsauran mataki" a kasar ta Yemen.

Wani jami'in soja a jihar ta Ibb da ya nemi a boye sunansa, ya ce jiragen saman soja na kasar Saudiyya, da na sauran kawayenta sun lalata wata ma'ajiyar kayayyakin masarufi ta kungiyar Houthi, baya ga fararen hula wadanda harin ya hallaka su 24. Kaza lika jiragen saman sojan su kai farmaki kan sansanin tsaron mayakan dake wajen birnin Sanaa, fadar mulkin kasar ta Yemen.

Mutanen da suka ganewa idanunsu aukuwar lamarin sun bayyana cewa, an fara kai hare-haren ne tun daga safiyar Talata, a wani yunkuri na lalata dakin ajiye boma-bomai na sansanin sojojin sama, wanda kuma ya fashe a sakamakon farmaki.

Ya zuwa yanzu dai babu cikakken rahoto game da yawan mutanen da harin ya hallaka. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China