in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen UAE, Saudiya da Bahrain sun janye jakadunsu daga Qatar
2014-03-06 10:55:42 cri

A jiya Laraba ne kasashen hadaddiyar daular Larabawa (UAE), Saudiya da kuma Bahrain suka bayar da sanarwar janye jakadunsu daga kasar Qatar, bisa ga abin da suka kira rashin martaba ka'idojin kungiyar kasashen da ke yankin Gulf (GCC).

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da kasashen uku suka bayar, sun bayyana cewa, sun yanke shawarar daukar wannan mataki ne kan abin da suka kira kare harkokin tsaro da zaman lafiya a kasashen nasu.

Sun kuma bayyana cewa, har yanzu kasar ta Qatar ba ta aiwatar da yarjejeniyar tsaron kungiyar kasashen yankin na Gulf da aka sanya hannu a kai a watan Nuwamban shekarar da ta gabata ba, yarjejeniyar da take nufin karfafa hadin gwiwar tsaron da za ta magance sabbin barazanar da kasashen da ke shiyyar ke fuskanta.

Bugu da kari kasahen uku, sun bayyana cewa, sun yi kokarin shaidawa kasar ta Qatar da kada ta tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashe mambobin kungiyar, kamar yadda suka sanya hannu a cikin yarjejeniyar, amma kasar ta Qatar ba ta martaba wannan yarjejeniya ba.

Har ila yau, sun bukaci Qatar da kada ta goyi bayan duk wani bangaren da zai kawo barazanar tsaro da zaman lafiya ga kasashe mambobin kungiyar, inda suka ce, Qatar din tana taimakawa kungiyar 'yan uwa musulumi da aka haramta a galibin kasashen na yankin Gulf. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China