in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 2 suka mutu kuma 68 suka jikkata yayin arangama a Saudiya
2013-11-11 13:49:08 cri

Hukumomin 'yan sandan kasar Saudiya sun bayyana a ranar Lahadi cewa, mutane biyu, 'dan kasar Saudiya guda da 'dan wata kasar da ba'a tantance suka mutu yayin da 68 suka jikkata a wata arangama da jami'an tsaro a ranar Asabar a birnin Riyad, a cewar kamfanin dillancin labarai na kasar Saudiya.

A cewar kakakin 'yan sandan birnin Riyad, rikicin ya barke a yayin da wasu mutane da ba'a tantance su ba da ake zargi da hannu a kan wasu tashe-tashen hankali da suka faru a wasu hanyoyin babban birinin na Makka ta hanyar kai hare-hare da duwatsu da wasu ababe masu tsini a kan jama'a.

A cewar gidan talabijin na Al Arabia, 'yan kasar Habasha ne dake aiki ba bisa doka ba suka aikata wadannan ayyuka na tada zaune tsaye domin hana kamen su da ake bisa matakin da kasar ta dauka na farautar baki 'yan kasashen waje dake aiki cikin kasar ba bisa doka ba bayan karshen wa'adin ahuwar watanni shida da za ta kare a farkon wannan shekara.

Kakakin 'yan sandar ya bayyana cewa, an kame mutane 561 dake da hannu kan zanga-zangar tare da wasu mutanen da ba'a tantance ba.

A cikin mutanen da suka jikkata, akwai 'yan kasar Saudiya 28 da bakin waje 40, haka kuma an lalata motoci 104, in ji wannan jami'i. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China