in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ina lura da kin karbar kujerar mamban kwamitin sulhu na MDD da Saudiya ta sanar, in ji Ban Ki-moon
2013-10-19 17:20:19 cri
Ranar 18 ga wata, Ban Ki-moon, babban magatakarda na MDD ya ce, ya samu labarin cewa, kasar Saudiya ta ki karbar kujerar kwamitin sulhu ta karbar-karba ta MDD, sai dai yanzu bai samu rahoton hakan a hukumance ba. Sa'an nan ya ce, zai ci gaba da baiwa wannan lamari kulawar da ta dace.

A ranar 17 ga wata ne a yayin babban taron MDD karo na 68, aka zabi kasashen Saudiya, Chadi, Lithuania, Nijeriya da Chile don su zama sabbin mambobin kwamitin sulhu na MDD daga shekarar 2014 zuwa 2015, inda bayan wani dan lokaci, ma'aikatar harkokin wajen kasar Saudiya ta ba da wata sanarwar da ke cewa, sakamakon gazawar kwamitin sulhu wajen warware rikicin kasa da kasa, da raba kafa dangane da ra'ayinsa kan batutuwan Palasdinu da Isra'ila, da rikicin kasar Syria, gami da kawar da manyan makaman kare dangi a yankin Gabas ta Tsakiya da sai sauransu, ya nuna kwamitin sulhu bai sauke nauyin kiyaye zaman lafiya a duniya yadda ya kamata ba, don haka kasar ta Saudiya ta ki karbar kujerar.

A ranar 18 ga wata da safe, bayan da Ban Ki-moon ya halarci muhawarar kwamitin sulhu dangane da harkokin mata, da tafiyar da harkoki bisa doka, aiwatar da dokoki a lokacin wucin gadi a yayin rikici, ya bayyana wa 'yan jarida cewa, ya lura da labarin da aka bayar dangane da kin karbar wancan matsayi da Saudiya ta yi na kujerar kwamitin sulhu na karba-karba, amma bai samu rahoton a hukumance ba tukuna.

Har wa yau kuma, Ban ya karfafa gwiwar dukkan kasashe mambobin MDD, yana kira gare su da su shiga cikin ayyukan muhimman sassan majalisar daga dukkan fannoni, tare da kokarin kyautata hanyoyin da wadannan sassan majalisar suke bi wajen gudanar da ayyuka. Ya ce, majalisar na fatan inganta hadin gwiwa a tsakaninta da Saudiya, musamman ma wajen daidaita manyan kalubaloli tare, kamar rikicin Syria, da batun kafa kasar Palasdinu, da kuma yaki da ta'addanci.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China