in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saudiyya ta haramtawa jirgin shugaban kasar Sudan keta sararin samanta
2013-08-05 13:27:17 cri

Kasar Saudiyya ta haramtawa jirgin sama dauke da shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ikon keta sararin samanta, yayin da shugaban ke kan hanyarsa zuwa Tehran, babban birnin kasar Iran don halartar bikin rantsuwar sabon shugaban Iran din Hassan Rouhani, wanda aka gudanar a ranar Lahadi.

Rahotanni daga kamfanin dillancin labaran SUNA sun nuna cewa, hana wannan jirgi na shugaba Al-Bashir gitta sararin saman kasar ta Saudiyya, ya sanya shi ala tilas komawa, duk kuwa da cewa, jirgin na da iko irin na yada zango a kasar ta Saudiyya.

Yanzu haka dai Sudan din na jiran bayyani kan wannan lamari daga mahukuntan kasar ta Saudiyya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China