in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Pakistan
2015-04-21 20:26:30 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Pakistan Mamnoon Hussain a ranar talatan nan 21 ga wata a birnin Islamabad hedkwatar kasar.

A wannan rana da safe, bayan da Mr Xi ya gabatar da jawabi a majalisar dokokin Pakistan, ya tafi fadar shugaban kasar da firaministan kasar Mian Muhammad Nawaz Sharif ya rufa masa baya.

Yayin ganawar, Mr Xi ya ce, ziyarar da shugaba Mamnoon Hussain ya yi sau biyu a kasar Sin a shekarar bara ya kasance karo na farko da shugaban wata kasa ya kawo ziyara a nan kasar Sin bayan bikin sabuwar shekarar Sin bisa kalandar gargajiya, abinda yasa shugaban Sin ya mai da kasar Pakistan zangon farko a cikin ziyarar sa ta farko a wannan shekara, matakin da ya bayyana dankon zumunci dake tsakanin Sin da Pakistan. A saboda haka shugaba Xi yace yana fatan zurfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta wannan ziyara da kuma habaka hadin gwiwa tskaninsu nan gaba ta yadda za a amfana jama'ar kasashen biyu.

A nasa bangare kuma, Mamnoon Hussain ya ce, jama'ar kasar sa na sa ran sosai ga ziyarar shugaba Xi a kasarsu, kuma na fatan Mr Xi zai sami nasara sosai a wannan karo, shi kuma ya nuna godiya sosai ga taimakon da Sin take bayar a fannoni daban-daban ga kasarsa. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China