in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Yada ra'ayin Bandung a sabon zamani
2015-04-21 15:17:21 cri

Yanzu haka dai ana ci gaba da gudanar da taron shugabannin kasashen Asiya da Afirka, da bikin tunawa da cika shekaru 60 na taron Bandung, a biranen Jakarta da Bandung na kasar Indonesia, tarukan da za su gudana tsakanin ranakun 19 zuwa ta 24 ga watan nan da muke ciki an musu lakabi da "Kara hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, da tabbatar da zaman lafiya da walwala a duniya".

Shekaru 60 da suka gabata ne aka kira taron shugabannin kasashen Asiya da Afirka, a wani mataki na neman 'yanci da mulkin kai bai daya.

Zuwa yanzu dai yawancin kasashen sun samu 'yancin kansu, sai dai akwai wasu da ba su samu cikakken mulkin kai ba tukuna, da 'yanci a fannin tattalin arziki ba tukuna, inda maganar ci gaba ke kasancewa wani babban kalubalen da ake fuskanta. Bisa la'akari da wannan yanayin da ake ciki ne a wajen sabon taron shugabannin kasashen Asiya da Afirka da ke gudana yanzu, ba ya ga harkokin siyasa, za kuma a maida hankali ga batun kara lurawa da batun raya tattalin arziki, ta yadda ra'ayin Bandung da aka cimma shekaru 60 da suka wuce zai zamo mai sabuwar ma'ana.

Don gane da taron da ke gudana, wani masanin harkokin da suka shafi kudanci, da kudu maso gabashin Asiya na kasar Sin mai suna Zhang Xuegang, ya ce,"Wani babban ci gaban da aka samu wajen taron shugabannin kasashen Asiya da Afirka na wannan karo shi ne, baya ga musayar ra'ayi a fannin neman cimma daidaito, ana kuma kokarin daukar hakikanin mataki na hadin gwiwa. Hakan ya kasance wani sauyi mai nagarta, kasancewar ana bukatar shirye-shiryen da za a iya gudanar da su."

A gefen taron shugabannin kasashen Asiya da Afirka dake gudana kuwa, za a kira taron manyan kusoshi a fannin kasuwanci na kasashen Asiya da Afirka karo na 2, inda shugabanni na kasashe daban daban za su gabatar da jawabai, na sa kaimi ga hadin kan da ake yi tsakanin kasashen Asiya da na Afirka. Dangane da sakamakon da za a iya samu wajen taron, mista Xu Liping, wani mai nazarin al'adu na yankin Asiya da tekun Pasific, ya yi hasashen cewa, "Mai yiwuwa ne a matsayin wani muhimmin mataki, za a kafa wata cibiyar musamman mai kula da harkoki masu alaka da nahiyoyin Asiya da Afirka, ta yadda za a sanya taron shugabannin kasashen Asiya da Afirka zama wata zaunanniyar hukuma. Haka kuma, za a iya mai da taron shugabanni a fannin kasuwanci ya zama wani taro na shekara-shekara."

A taron Bandung da ya gudana shekaru 60 da suka wuce, an gabatar da ra'ayin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa a karon farko, lamarin da ya bude hanyar taimakawa juna tsakanin kasashen dake kokarin neman bunkasar tattalin arzikinsu. Zuwa watan Fabrairu na shekarar 2005, an zartas da "Sanarwar kulla sabuwar huldar abokai mai alaka da manyan tsare-tsare, tsakanin nahiyoyin Asiya da Afirka". A yayin wani taron shugabannin kasashen nahiyoyin 2 da aka kira a kasar Indonesia, an aza tubali ga kokarin hadin gwiwa tsakanin nahiyoyin Asiya da Afirka musamman ma a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da al'adu.

Sai dai sakamakon wasu dalilai, nahiyoyin 2 na ci gaba da fuskantar wasu matsaloli ta fuskar raya tattalin arziki da daidaita zaman al'umma a yanzu, ta yadda suka gaza zama masu-fada-a-ji yayin da suke hulda da kasashe masu sukuni. Bisa wannan yanayin da ake ciki ne kuma, shugabanni masu halartar taron na wannan karo, za su gabatar da wata sanarwa ta "farfado da huldar abokai da ta shafi manyan tsare-tsare tsakanin nahiyoyin Asiya da Afira", don tanadin ayyukan da za a yi a nan gaba a fannin hadin gwiwa tsakanin nahiyoyin 2.

Dangane da wannan sabon shirin da za a gabatar, mista Xu Liping ya ce, za a mai da hankali sosai ga hadin gwiwar da ake yi a fannin gina ababen more rayuwa."Shirin zirin tattalin arziki na siliki da hanyar Siliki ta ruwa na karni na 21 da kasar Sin ta gabatar, musamman ma batutuwan da aka bayyana cikin shirin wadanda suka shafi aikin gina ababen more rayuwar jama'a, sun kasance wani babban fannin da za a kula da shi, a kokarin raya kasashen Asiya da Afirka. Sakamakon rashin fasahohin zamani da kudi, kasashen Asiya da Afirka na fuskantar matsalar karancin kayayyakin more rayuwa. Yayin da kasar Sin ke ba da fifiko a wannan fanni, wanda za ta iya amfani da shi don samar da moriya ga sauran kasashen dake nahiyoyin Asiya da Afirka."

Ban da haka, a cewar mista Xu Liping, ya kamata a kara mu'amalar mutane tsakanin kasashen dake nahiyoyin Asiya da Afirka don kara fahimtar juna, da kau da wasu ra'ayoyi marasa amfani wadanda ke da alaka da huldar dake tsakaninsu. Sa'an nan kamata ya yi, a habaka hadin gwiwar da ake yi a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da al'adu tsakanin nahiyoyin 2, don cimma burinsu na samun ci gaba tare. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China