in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin raya "ziri daya da hanya daya" da Xi Jinping ya gabatar na da babbar ma'ana ga ci gaban kasar Sin
2014-10-11 09:15:57 cri

Yau sama da shekara daya da ta gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shirin raya "zirin tattalin arziki dake kan hanyar siliki" da "sabuwar hanyar siliki dake kan teku na karni na 21". Ko da aka fitar da wannan manufa, sai nan da nan ta jawo hankulan kasashen duniya sosai, wadda kuwa ta samu goyon baya daga kasashen da manufar ta shafa, gami da karfafa kwarin gwiwar larduna da biranen kasar Sin masu ruwa da tsaki. Hakan ya sheda babban tasirin da manufar ta bayar a duniya. Daga baya kuma a cikin wannan shekarar da muke ciki, kasar Sin da kasashe da kungiyoyin shiyya-shiyya da batun ya shafa sun kirkiro salon hadin kansu, gami da yin namijin kokarin wajen raya wannan "ziri daya da hanya daya", wanda ya samu babban ci gaba. 

Shirin raya "zirin tattalin arziki dake kan hanyar siliki" da "sabuwar hanyar siliki dake kan teku na karni na 21" da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar yau da shekara guda da ta gabata, wani babban shiri ne mai hangen nesa, sannan kuma wani babban sha'ani ne da zai kawo alheri na a zo a gani ga jama'a, wanda zai shimfida wata hanyar samun bunkasuwar kasa da kasa gaba daya cikin lumana. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ba kawai ya gaji ruhun tsohuwar hanyar siliki ba, wato hadin gwiwa da amincewar juna, zaman daidai wa daida da moriyar juna, yin hakuri da koyi da juna don samun nasara tare, a'a har ma ya dace da yanayin zamanin yau na karni na 21, wato zaman lafiya da hadin gwiwa don samun ci gaba da nasara gaba daya. Ban da wannan shirin ya hada burin kasar Sin da na duniya yadda ya kamata, don haka yana da babbar ma'ana ga duk duniya bisa manyan tsare-tsare.

Idan an cimma shirin "ziri daya da hanya daya", to za a samu hanyar tattalin arziki mai karfi a asirce da za ta shafi kasashe da dama, wadda za ta amfana wa mutane biliyan 4.4, jimillar kudaden da za a samu ta GDP kuwa za ta kai dala biliyan 21,000, wadannan jimilolin biyu kuwa za su kai kashi 63 da kashi 29 cikin kashi dari bisa na duk duniya. Bugu da kari, yankin da wannan shiri ya shafa yanki ne mai saurin ci gaban tattalin arziki, wanda ya kunshi yawan kasashe masu tasowa da masu saurin bunkasuwa, wadanda ke da kyakkyawar makoma wajen samun ci gaba. Kasar Sin ta hada kai sosai tare da wadannan kasashe, matsakaiciyar jimillar cinikayya a cikin wadannan shekaru 10 da suka gabata ta karu da kashi 19 cikin kashi dari a ko wace shekara.

Ya zuwa yanzu dai, hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da wadannan kasashe ta samu babban ci gaba bisa kokarin da suka yi a cikin shekarar da ta gabata, musamman ma a fannoni zirga-zirga, cinikayya, zuba jari, makamashi, albarkatu, tsaron sha'anin kudi da dai sauransu.

Da farko dai, bisa tsarin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai SCO, da kungiyar Sin da kasashe 10 na ASEAN, da kungiyar BRICS, da kuma kyakkyawar dangantaka a tsakanin kasar Sin da Rasha, da kasashen da ke Turai ta Tsakiya, Asiya ta Tsakiya, Gabas ta Tsakiya, da kuma kudancin Asiya, Sin da kasashen da ke kan hanyar siliki sun kafa sabon tsarin hadin kansu.

Ban da wannan kuma, bisa wannan shiri, kasashen da ke kan hanyar siliki na shirin kafa tsarin zirga-zirga da ya shafi kasa, teku da kuma sama. Haka zakila, ana shirin kafa bankin zuba jari don tuntubar juna na Asiya, asusun raya kungiyar SCO, da kuma bankin raya kungiyar SCO domin mara baya ga raya muhimman ayyukan more rayuwa, sai dai duk wadannan za'a kafa su ne a shekara mai zuwa.

Bugu da kari kuma, bisa wannan shiri, ana raya cibiyoyin rarraba kayayyaki da yankunan cinikayya cikin 'yanci na yankunan da ke kan hanyar siliki, a kokarin kara azama ga wadatar tattalin arziki, ci gaban zaman al'umma, tsaron shiyya-shiyya a kasashen da shirin ya shafa. Hakan a karshe dai za a cimma burin sa kaimi ga harkokin siyasa bisa karfin tattalin arziki, da kuma inganta aikin kiyaye zaman lafiya bisa karfin harkokin siyasa.

Ko shakka babu, ba kawai shirin "ziri daya da hanya daya" babban shiri ne na farfadowar al'ummar Sin ba, hatta ma kyakkyawar hanya ce da kasashen da ke kan hanyar siliki ke bi wajen samun wadata, wanda ya hada burin kasar Sin da na duniya baki daya. Shirin kuwa zai ba da taimako wajen kyautata dangantaka a tsakanin kasa da kasa da ke kan hanyar siliki, da samun kwanciyar hankali ta fuskar siyasar da ta shafi yankunan da wasu kasashe ke kasancewa, da ci gaban tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama'a. Haka zakila, shirin zai taimaka wajen inganta hadin gwiwar kasa da kasa bisa fifikonsu, ta yadda kasashen za su kasance al'ummomin da ba'a iya rarraba su saboda yadda moriyarsu da kaddararsu suka zo daya.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China