in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manufar da Xi Jinping ya tsara dangane da huldar dake tsakanin Sin da Amurka
2014-10-10 10:58:19 cri

Tun bayan da mista Xi Jinping ya zama shugaban kasar Sin a shekarar 2013, kasar ta kara daukar wasu matakai masu yakini a fannin hulda da kasashen waje, musamman ma ta la'akari da yadda take kokarin kare 'yancin kanta.

Bayan da kasar Sin ta sanar da kebe wani yanki na tsaron sararin samaniya a yankin tekun dake gabashin kasar a watan Nuwamba na shekarar 2013, ya sa shugabannin kasar Amurka suka kara nuna mugun fata game da huldar dake tsakanin kasashen 2, hakan ya sa Amurka ta kara daukar tsattsauran matsayi yayin da take hulda da kasar Sin, musamman ma ta la'akari da wasu matakan da ta dauka kan harkokin da suka shafi yankin tekun dake kudancin kasar Sin.

Sai dai idan mun yi cikakken nazari kan jawaban da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar tun bayan da ya gana da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama a watan Yuni na shekarar 2013, za mu gano cewa, hakika kasar Sin ba ta sauya munufarta ba, ganin yadda take ci gaba da kokarin neman ci gaba ta hanyar zaman lafiya. Kana a fannin hulda da kasar Amurka, kasar Sin tana kokarin kafa wata sabuwar dangantaka da ta dace da matsayin kasashen 2 na wata kasa babba.

Kasar Sin ta tsara munafarta dangane da kasar Amurka ne bisa wani tushen ra'ayi, wato a wannan zamanin da tattalin arzikin duniya ke dunkulewa waje guda, kuma zaman lafiya da neman ci gaba ke zama babban jigon zamanin, huldar dake tsakanin Sin da Amurka ta ci gaba da kasancewa dangantaka mafi muhimmanci a kokarin Sin na hulda da kasashen waje. Duk da cewa an samu rikici tsakanin manyan kasashe a tarihin dan Adam, amma a ganin shugabannin kasar Sin, kasahen Sin da Amurka za su iya magance haka, kamar yadda shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, 'tekun Pasific mai girma zai iya kunsar kasashen Sin da Amurka su biyu duka'. Sa'an nan dangane da hanyar da za a bi don kulla sabuwar dangataka tsakanin kasashen 2, shugaban ya gabatar da manufofi 3, wato ' a bar rikici da juna'. da 'girmama juna', da kuma 'yin hadin gwiwa don samun moriya tare'.

Da farko, an gabatar da shawarar ' a bar rikici da juna' ne, ganin yadda Sin da Amurka ba su yi amince da juna sosai ba. Saboda haka bangaren Sin ta yi kira da a karfafa aminci da fahimtar juna tsakanin kasashen 2 bisa hanyoyi daban daban, da suka kunshi mu'ammalar shugabanninsu, da yin amfani da wasu dama kamar su taron tsakanin kasashen 2 a fannin manyan tsare-tsare da tattalin arziki, da cudanya ta fuskar al'adu da aikin soja, ta yadda bangarorin 2 za su iya kara hira da juna don neman fahimtar niyyar su da tabbatar da matakan da za su dauka a nan gaba. A karshe za a iya daidaita sabanin ra'ayi tsakaninsu, ta hanyar shawarwari da hadin gwiwa, maimakon rikici da juna.

Sa'an nan, game da shawarar da shugaba Xi ya gabatar ta 'girmama juna', hakan na nufin a lura da moriyar kasashen 2 da bukatunsu. Burin kasar Sin, a cewar shugaba Xi Jinping, ita ce a girmama ta kan 'yancin kanta, da tsarin zaman al'umma da hanyar raya kasa da ta zaba. Ya kamata kasashen 2 su yi kokarin cimma matsaya daya, da daidaita bambancin ra'ayi , gami da hakuri da koyi da juna. Dangane da manufofin kasar Amurka, kasar Sin ta kalubalanci Amurka da ta girmama 'yancin kan kasar Sin da niyyarta ta kiyaye cikakken yankin kasa, da bar nuna goyon baya ga 'yan barakan kasar. Haka kuma game da wasu matsalolin da aka samu a yankunan tekun kasar Sin, kasar ta bukaci Amurka da ta nuna adalci da sanin ya kamata, don taimakawa kokarin sassanta yanayi da daidaita matsalolin da ake fuskanta. Sa'an nan a fannin hakkin dan Adam, kasar Sin ta san tabbas ne za a samu bambancin ra'ayi tsakaninta da kasar Amurka, ganin yadda kasashen 2 suke da yanayin kasa da tarihi na daban, amma ya kamata kasar Amurka ta girmama hanyar da kasar Sin ta zaba, da kokarinta na neman ci gaba a wannan fanni.

Ban da haka kuma, sai shawarar kasar Sin ta 3, wato 'kokarin hadin kai da tabbatar da moriyar juna', hakan a ganin kasar Sin shi ne sharadin da za a cimma kafin a samu damar kulla sabuwar dangantaka tsakanin manyan kasashen 2. Kamata ya yi bangarorin 2 su yi kokari na kula da moriyar juna maimakon nuna son kai, domin kasashen Sin da Amurka suna da moriya daya a wurare daban daban, idan daya ya ji rauni, dayan ma ba zai ji dadi ba. Don haka ya kamata su yi kokarin hadin gwiwa da juna a wasu batutuwa masu janyo hankalin jama'ar duniya, kamarsu batun nukiliya na zirin Koriya da Iran, da sauyin yanayin duniya, da yaki da ta'addanci, da tsaron yanar gizo ta Intanet, da aikin makamashi, da dai matakantansu.

Haka zalika, dangane da matsalar rashin daidaituwa kan cinikayyar da ake yi tsakanin Sin da Amurka, kasar Sin na ganin cewa, ya kamata kasar Amurka ta yi kwaskwarima kan manufofinta da tsarin kasar a fannin tattalin arziki, da soke kayyadewa da aka sanya ma kayayyakin da za a iya fitar zuwa kasar Sin. Sa'an nan a fannin cudayar sojojin kasashen 2, kasar Sin ta nuna niyyarta ta karfafa mu'ammala tsakanin hafsoshi masu matsayi daban daban, kuma a fannoni daban daban, da kara yin atisayen soja da hadin gwiwa.

Hakika yankin Asiya da tekun Pasific shi ne wurin da ya fi janyo hankalin kasashen Sin da Amurka a yunkurin su na kare moriyar kasa. Dangane da batutuwan da suka shafi wannan yanki, kasar Sin tana ganin cewa, kasashen biyu suna samun moriyar bai daya sosai, wadda ta fi bambancin ra'ayi da ake samu tsakaninsu. Har ila yau, kasar Sin ta riga ta canza dabarar da ta saba da dauka ta mayar da martani ga tsokanan kasar Amurka, inda ta fara daukar wasu matakai masu yakini. Ga misali, shugaba Xi Jinping ya gabatar da wani sabon ra'ayin tsaron yankin Asiya a wani taron shugabannin da aka kira a watan Mayun da ya gabata don tabbatar da aminci a zukatan jama'ar kasashen Asiya, inda aka yi watsi da nuna fin karfi, maimakon haka an rike ra'ayi na yin hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban don neman tabbatar da tsaro irin na bai daya kuma mai dorewa. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China